Jerin Sunayen Mutum 14 Da Suke Neman Gaje Kujerar Gwamna Malam El-Rufai a 2023

Jerin Sunayen Mutum 14 Da Suke Neman Gaje Kujerar Gwamna Malam El-Rufai a 2023

  • Hukumar zaɓe ta ƙasa ta saki sunayen yan takarar gwamnan jihar Kaduna da zasu fafata a babban zaɓen 2023
  • Sanata Uba Sani, Isah Ashiru Kudan, Sulaiman Hunkuyi da wasu yan takara 14 sun shiga jerin sunayen INEC na ƙarshe
  • Wannan na zuwa ne yayin da rage ƙasa da watanni Shida gabanin babban zaben 2023

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta fitar da jerin sunayen 'yan takarar gwamnan jihar Kaduna na ƙarshe da zasu fafata a babban zaɓen 2023 da ke tafe.

Jaridar Tribune Online tace sabbin sunayen da INEC ta saki ranar Laraba ya nuna soke tsohon jerin 'yan takara na baya kuma wannan karon kunshin na ɗauke da sunayen 'yan takara da mataimakansu.

Kara karanta wannan

INEC Ta Saki Sunayen Yan Takaran Gwamna Da Majalisar Jihohi Da Zasu Fafata a 2023

Hukumar zaɓe INEC.
Jerin Sunayen Mutum 14 Da Suke Neman Gaje Kujerar Gwamna Malam El-Rufai a 2023 Hoto: tribuneonline
Asali: UGC

Daftarin sunayen ya nuna cewa hukumar zabe ta amince da Jonathan Asake, a matsayin ɗan yakarar gwamnan Kaduna a inuwar Labour Party.

Kafin INEC ta saki sunayen, Sanata Uba Sani da yan tawagarsa na ɗar-ɗar din cewa mai yuwuwa hukumar ta ƙi amince wa da shi a matsayin ɗan takarar gwamna a inuwar APC.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hakan ta faru ne sakamakon ɗaya daga cikin 'yan takarar da suka nemi tikitin APC, Hon. Muhammed Sani Sha'aban, ya ƙalubalanci nasarar Uba Sani a Kotu.

A ƙarar da ya shigar gaban babban Kotun tarayya mai zama a Kaduna, Sha'aban ya yi ƙarar Jam'iyyar APC, Uba Sani da INEC a matsayin na ɗaya na biyu da na uku.

Legit.ng Hausa ta gano cewa ana tsammanin Kotun zata cigaba da sauraron ƙarar mako mai zuwa ranar Laraba.

Kara karanta wannan

2023: A Kwana 90 Zan Dawo Da Zaman Lafiya a Katsina, Ɗan Takarar PDP Ya Faɗi Abu 2 Da Zai Sa Gaba

Jerin sunayen manyan yan takarar gwamnan Kaduna

Daga cikin sunayen yan takara 17 da zasu fafata kan kujerar gwamnan Kaduna sun haɗa da, Sanata Uba Sani (APC), Hon Isah Ashiru Kudan (PDP), da Sulaiman Utsman Hukunyi (NNPP).

Sauran sun haɗa da Hayatudden Lawal Maƙarfi (PRP), Jonathan Asake (LP), Sen. Caleb Zagi (ADC), Dakta Andrew Duya (APGA) da Ibrahim Adamu (SDP) da sauran su.

A wani labarin kuma mun kawo muku Nasihar da Shugaba Buhari Ya Yi Wa Yan Takarar Shugaban Kasa 18 a Wurin Taron Abuja

Shugaba Buhari ya gargaɗi 'yan takarar shugaban kasa 18 su guji kalaman fusata jama'a yayin kamfen 2023.

A wurin taron sa hannu kan zaman lafiya, Buhari ya roki masu neman gaje kujerarsa su nemi kuri'un jama'a ta hanya mai tsafta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel