INEC Ta Fitar da Sunayen 'Yan Takarar Shugaban Kasa da Mataimakansu Na Karshe Gabanin 2023

INEC Ta Fitar da Sunayen 'Yan Takarar Shugaban Kasa da Mataimakansu Na Karshe Gabanin 2023

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta fitar da cikakken jerin sunayen yan takara da jam'iyyu suka tsayar, waɗan da zasu fafata a babban zaɓen 2023 dake tafe.

Domin biyayya ga dokar sashi na 32 (1) dake ƙunshe a kundin dokokin zaɓe 2022, INEC ta saki jerin yan takarar wanda ya ƙunshe sunayen masu neman shugaban kasa, Sanatoci da mambobin majalisar tarayya.

INEC ta sanar da fitar da sunayen ne a wata sanarwa da ta sa a shafinta na dandalin sada zumunta wato Tuwita.

Farfesa Mahmud Yakubu.
INEC Ta Fitar da Sunayen 'Yan Takarar Shugaban Kasa da Mataimakansu Na Karshe Gabanin 2023 Hoto: premiumtimesng
Asali: UGC

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa daftarin ya ƙunshi sunaye, sunan jam'iyya, yawan shekaru, jinsi da kuma shaidar karatu na dukkanin 'yan takarar kuma hukumar ta fitar da su kwanaki 156 dai-dai kafin ranar zaɓen 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Haka zalika, hukumar ta manna sunayen yan takarar da mataimakansu 36 na jam'iyyu 18 da masu neman kujerun majalisun tarayya a babban Ofishin INEC dake Arewa 10, Abuja.

Kara karanta wannan

ASUU: Kar Ku Kai Matasa Bango, Ba Zamu Iya Shawo Kansu Ba Idan Suka Tunzura, Wani Sarki Ya Gargaɗi Buhari

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Zaku iya ɗakko cikakken daftarin sunayen baki ɗaya nan; yan takarar 2023.

Yan takarar shugaban kasa.
INEC Ta Fitar da Sunayen 'Yan Takarar Shugaban Kasa da Mataimakansu Na Karshe Gabanin 2023 Hoto: INEC
Asali: UGC

Yan takarar shugaban kasa.
INEC Ta Fitar da Sunayen 'Yan Takarar Shugaban Kasa da Mataimakansu Na Karshe Gabanin 2023 Hoto: INEC
Asali: UGC

Yan takarar shugaban ƙasa.
INEC Ta Fitar da Sunayen 'Yan Takarar Shugaban Kasa da Mataimakansu Na Karshe Gabanin 2023 Hoto: INEC
Asali: UGC

Manyan yan takara

Daga cikin yan takarar da sunayensu suka fita a daftarin sun haɗa da, tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, na jam'iyyar PDP da tsohon gwamnan Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC.

Haka nan ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, da tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na jam'iyyar NNPP mai kayan marmari.

A wani labarin kuma Abba Gida Gida Ya Nesanta Kansa da Bidiyon Neman Kuɗin Kamfen na zaɓen gwamnan Kano a 2023

Abba Gida Gida, mai neman kujerar gwamnan Kano a inuwar NNPP ya nesanta kansa da wani Bidiyo dake yawo a kafafen sada zumunta.

A wata sanarwa da kakakinsa ya fitar, Abba ya nemi ɗaukacin al'umma musamman mambobin NNPP su yi fatali da Bidiyon.

Kara karanta wannan

Sunayen Tsofaffin Shugabannin Rundunar Soji Uku da Zasu Yi Wa Atiku Kamfe a 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel