2023: Wani Jigon PDP da Shugabannin Gdunduma Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Kebbi

2023: Wani Jigon PDP da Shugabannin Gdunduma Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Kebbi

  • Yayin da PDP ke shirin yaƙin neman zaɓen shugaban kasa, a jihar Kebbi jam'iyyar ta gamu da sabon ƙalubalen sauya sheka
  • Wani mamba a yankin Danko Wasagu, Hon. Junaidu Wasagu, da shugabannin PDP na gundumomi sun sauya sheka zuwa APC
  • Ana ganin dai rashin mambobi irin haka wani ƙalubale ne ga ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar

Kebbi - Wani jigon jam'iyyar PDP a yankin ƙaramar hukumar Danko-wasagu, Hon. Junaidu Wasagu, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC tare da baki ɗaya shugabannin gundumumonin yankin.

Wasagu ya shaida wa yan jarida a Sakatariyar APC da ke Birnin Kebbi cewa sun ɗauki matakin barin PDP ne saboda rashin adalci da daidaito da aka nuna musu, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Tambarin PDP.
2023: Wani Jigon PDP da Shugabannin Gdunduma Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Kebbi Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Ya kara da cewa nasarorin da gwamnatin Atiku Bagudu ta samu na gaban kwatance da ayyana, Dr Nasir Idris Kauran Gwandu a matsayin ɗan takarar gwamna sun taka rawa wajen yanke sauya shekarsu zuwa APC.

Kara karanta wannan

Yadda Kwankwaso Zai Lallasa Atiku a Arewa, Ya Ba Da Mamaki a Zaɓen 2023, Tsohon Ɗan Majalisa

Haka zalika, Honorabul Wasagu ya tabbatar da cewa zai yi biyayya ga gwamna da sauran shugabannin APC domin ganin baki ɗaya yan takarar jam'iyyar sun ɗare madafun ikon a zaɓe mai zuwa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Zamu yi aiki tare - Shugaban APC

Shugaban jam'iyyar APC reshen jihar Kebbi, Alhaji Abubakar Mohammed Kana Zuru, ya tabbatar wa Honorabul Wasagu da yan tawagarsa cewa yanzu an zama ɗaya.

A cewarsa, jam'iyyar APC mai mulki zata jawo su a jiki wajen gudanar da dukkanin harkokin jam'iyya ba tare da nuna musu bambanci ba.

A wani labarin kuma Tsohon hadimin gwamna da wasu mambobi sama da 13,000 sun sauya sheka daga APC zuwa PDP a Kaduna

Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Kaduna ta gamu da gagarumar matsala yayin da ake shirin tunkarar babban zaɓen 2023.

Tsohon hadimin gwamna, Hon. Wilson Yangye da wasu mambobin sama da 13,000 sun koma PDP a kudancin jihar.

Kara karanta wannan

Atiku da Wike: Tabbas Zamu Warware Rikicin PDP Gabanin Zaɓen 2023, Sabon Shugaban BoT

Asali: Legit.ng

Online view pixel