2023: Atiku Ba Zai Kama Kafar Kwankwaso Ba a Arewa, Tsohon Dan Majalisa

2023: Atiku Ba Zai Kama Kafar Kwankwaso Ba a Arewa, Tsohon Dan Majalisa

  • Abdulmumini Jibrin yace tsohon gwamnan Kano, Kwankwaso, na da damar lashe zaɓen shugaban kasa a 2023
  • Tsohon ɗan majalisar yace Atiku na jam'iyyar PDP ba zai kama kafar Kwankwaso ba wajen samun kuri'u a arewacin Najeriya
  • Jibrin yace ba'a maganar APC domin jam'iyyar ta samu nasara ne saboda kuri'u miliyan 12m na Buhari yanzu kuma babu

Abuja - Kakakin jam'iyyar NNPP mai kayan marmari, Abdulmumini Jibrin, yace ɗan takarar PDP, Atiku Abubakar, ba zai haɗa kansa da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ba.

Jibrin ya yi wannan furucin ne yayin wata hira a gidan Talabijin na Channels tv a shirin su na 'Siyasa a Yau.'

Abdulmumini Jibrin.
2023: Atiku Ba Zai Kama Kafar Kwankwaso Ba a Arewa, Tsohon Dan Majalisa Hoto: dailytrust.com

Tsohon ɗan majalisar tarayya yace Kwankwaso zai kwashe kafatanin kuri'un mutanen arewa kuma ya samu isassun ƙuri'un da ake bukata a kudancin Najeriya, kamar yadda Dailytrust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ruwan Wuta: Jirgin Yakin Soji Ya Halaka Bashir Iblis da Wasu Ƙasurguman Yan Ta'adda a Arewa

Yace, "Na ji ɗan uwana Daniel Bwala na ɓaɓatun cewa ko ina kaje akwai PDP, ta ya? A zaɓen 2015 an buga su da ƙasa ta ko ina, haka aka sake lallasa su a zaɓen 2019, tarihi zai maimaita kansa ne kawai a 2023."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ɗan takararsu na shugaban kasa (Atiku) ba zai kama ƙafar Kwankwaso ba wajen karɓuwa a arewacin Najeriya. Idan muka ɗauki APC, gaskiyar da basu kaunar a faɗa ita ce suna samun nasara a zaɓukan nan ne saboda Buhari."
"Kowane zaɓe APC na fara shi da kuri'u miliyan 12m a ƙasa saboda Buhari, amma yanzu wannan kuri'un da suke tutiya da su sun gushe."

Yadda Kwankwaso zai yi nasara a 2023

Jibrin ya ƙara da cewa a karo na farko cikin shekaru Takwas, jam'iyyar APC zata fara zaɓe babu kuri'a ko ɗaya saboda shugaba Buhari ya kauce.

Kara karanta wannan

2023: Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa, Rabiu Kwankwaso, Ya Yi Kus-Kus da Wani Gwamnan APC

"A karon farko cikin shekara 8 zasu fara zaɓen shugaban ƙasa ba kuri'a ɗaya, ina zasu lalubo kuri'u miliyan Takwas? Kalubalen jagororin APC kenan da basu kokarin magance wa."
"Zasu fara da babu, yanzu ka nuna mun mutum ɗaya a APC mai farin jinin da zai jawo waɗannan tulin kuri'un, ba zasu iya ba. Batun gaskiya Kwankwaso ya kulle ko ina a arewa kuma zai samu isassun ƙuri'u a kudancin ƙasar nan."

A wani labarin kuma Kwankwaso Ya Yi Zama na Musamman da Abdussalami da IBB a Minna

Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya ziyarci gidajen tsofaffin shugabannin Najeriya yayin da ya je jihar Neja.

Tsohon gwamnan Kano ya kai wa Janar Ibrahim Badamasi Babangida da Janar Abdusalam Abubakar ziyara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel