Zaben 2023: Kwankwaso Ya Yi Zama na Musamman da Abdussalami da IBB a Minna

Zaben 2023: Kwankwaso Ya Yi Zama na Musamman da Abdussalami da IBB a Minna

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya ziyarci gidajen tsofaffin shugabannin Najeriya yayin da ya je jihar Neja
  • ‘Dan takaran ya kai wa Janar Ibrahim Badamasi Babangida da Janar Abdusalam Abubakar ziyara
  • ‘Yan tawagar ‘dan takaran shugaban kasar sun hada da ‘dan takarar Gwamna, Ibrahim Sokodeke

Niger - Rabiu Musa Kwankwaso mai neman zama shugaban kasa a inuwar jam’iyyar NNPP ya kai ziyara zuwa wasu garuruwa a jihar Neja.

‘Dan takaran ya ziyarci Neja ne domin bude wasu daga cikin ofisoshin jam’iyyarsa mai alamar kayan dadi, yayin da ake shirye-shiryen zabe.

Daga nan Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi amfani da wannan dama, ya je gidan tsofaffin shugabannin da aka yi a lokacin mulkin soja.

Rabiu Kwankwaso ya kai wa Janar Ibrahim Badamasi Babangida da kuma Janar Abdusalam Abubakar ziyarar girmamawa a gidajensu.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Jonathan ya yi ganawar sirri tsoffin shugabanni 2 na Najeriya a Minna

Mai taimakawa tsohon gwamnan wajen yada labarai, Saifullahi Hassan ya tabbatar da wannan ganawa da ya fitar da hotuna a shafukansa.

Legit.ng Hausa ta ga hotunan ziyarar da ‘dan takaran shugaban kasar ya kai wa manyan kasar da aka wallafa a Facebook da Twitter.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso da Abdussalam
Abdusalam Abubakar, Rabiu Musa Kwankwaso da Gwamnan Neja Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Twitter

Jawabin da Hadimin Kwankwaso ya fitar

"A yau (15 ga watan Satumba 2022), ‘Dan takaran NNPP na zaben shugaban kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, PhD, FNSE ya kai ziyara ga Janar Abdusalam Abubakar da Janar Ibrahim Badamasi Babangida a gidajensu a Minna, jihar Neja.”

Gwamna ya yi wa Kwankwaso jagora

Kamar yadda Legit.ng Hausa ta fahimta, Gwamna Abubakar Sani Bello ne ya yi wa ‘dan takaran da tawagarsa iso zuwa wajen Abdusalam Abubakar.

Janar Abubakar wanda suruki ne a wajen Gwamnan Neja ya yi mulkin Najeriya na gajeren lokaci bayan rasuwar Janar Sani Abacha a shekarar 1998.

Kara karanta wannan

2023: Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa, Rabiu Kwankwaso, Ya Yi Kus-Kus da Wani Gwamnan APC

Shi kuwa Ibrahim Badamasi Babangida mai shekara 81 ya yi shugabanci na shekaru takwas bayan hambarar da gwamnati a 1985, ya sauka ne a 1993.

A tawagar Kwankwaso akwai irinsu Alhaji Ibrahim Mohammed Sokodeke mai takarar gwamna, Injiniya Buba Galadima, sai kuma wasu ‘yan wasa.

Wankin hula zai kai dare

A makon nan aka samu rahoto cewa Sanata Suleiman Othman Hunkuyi yace zaben shugaban kasan shekarar 2023 zai iya zuwa da abin ban mamaki.

‘Dan takarar gwamnan na Kaduna yana ganin babu ‘dan takarar da zai samu galaba a tashin farko, yana ganin watakila zaben zai je ga zagaye na biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel