Yanzu Yanzu: Duk Da Ziyarar Atiku, Makinde Ya Ce Dole Ayu Yayi Murabus

Yanzu Yanzu: Duk Da Ziyarar Atiku, Makinde Ya Ce Dole Ayu Yayi Murabus

  • Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya ce dole Sanata Iyorchia Ayu, ya yi murabus daga matsayin shugaban PDP na kasa
  • Makinde ya bayyana cewa PDP da Atiku Abubakar na son kawo sauyi a kasar nan don haka dole su fara kawo sauyi a jam'iyyarsu
  • Ya bayyana cewa ta hanyar saukan Ayu ne kadai mutanen yankin kudu maso yamma za su yarda cewa ana yi da su a cikin babbar jam'iyyar adawar

Oyo - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bukaci lallai shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party, Sanata Iyorchia Ayu, ya yi murabus daga kan kujerarsa.

Makinde ya ce ta haka ne mutanen kudu za su ji cewa lallai ana yi dasu a cikin babbar jam’iyyar adawar kasar.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Atiku ya sake kai ziyara jihar Kudu, ya samu tarbar gwamna Makinde

Gwamnan ya yi wannan kiran ne a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP a kudu maso yamma tare da dan takarar shugaban kasar jam’iyyar, Alhaji Atiku Abubakar.

Shugaban PDP na kasa
Yanzu Yanzu: Dole Ayu Ya Tattara Komatsansa Ya Koma Gida, In Ji Gwamnan PDP Hoto: Guardian
Asali: Facebook

Makinde da takwaransa na jihar Ribas, Nyesom Wike, sun taso PDP a gaba kan shugaban jam’iyyar na kasa da dan takarar shugaban kasa wadanda dukkaninsu yan arewa ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma, a jawabinsa na maraba, ya bayyana Atiku a matsayin “shugaban kasar Najeriya mai zuwa a 2023.”

Wannan kirari da Makinde ya yiwa Atiku ya sa wajen taron ya dauki babban tafi daga manyan shugabannin PDP da ke dakin taron.

Jam'iyyar The Cable ta nakalto Makinde na cewa:

“Magana ta gaskiya itace cewa bamu da kowace matsala imma da jam’iyyarmu ko dan takararmu. Idan akwai matsaloli dole a gabatar da su.
“Kamata yayi ace mu baiwa mutanenmu karfin gwiwa, muna so su sauraremu.

Kara karanta wannan

Rikicin Cikin Gida: Shugaban PDP ya Mika Mulki ga Mataimakinsa, Ya Bayyana Dalili

“Jam’iyyarmu na so ta ceto Najeriya kuma dan takararmu mai hadin kai ne. yana so ya sauya fasalin Najeriya.
“Shekaru takwas na jam’iyyar All Progressives Congress ya jefamu a halin rabuwa. Batun shine dole mu aikata abun da muke wa’azi akai. Idan muna son hada kan Najeriya, dole mu fara hada kan PDP tukuna.
“Idan muna so mu sauya fasalin Najeriya, dole ne mu kasance da niyyar kawo hadakar jam’iyyar PDP. Muna da karfin? Amsar ita ce eh.
“Sakon da ke fitowa daga PDP reshen kudu maso yamma shine kudu maso yamma na neman cewa ayi garambawul a kwamitin uwar jam’iyya na PDP.
“Muna neman shugaban jam’iyyar na kasa ya sauka don kudi ta shiga ayi da ita. Wannan ne sakon.”

Gwamna Makinde Ya Tarbi Atiku, Okowa, Mambobin NWC Na PDP, Da Sauran Jiga-Jigai

A gefe guda, mun ji cewa Gwamnan Seyi Makinde na jihar Oyo ya karbi bakuncin dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar a gidan gwamnatin jihar dake Agodi, birnin Ibadan.

Kara karanta wannan

Abin da Ya Sa Atiku Ya Yi Watsi da Wike, Ya Jawo Okowa Ya Zama Mataimakinsa

Atiku dira gidan gwamnatin na Oyo ne tare da abokin gaminsa a tafiyar 2023, Ifeanyi Okowa da misalin karfe 11:46 na safe.

Hadimin gwamnan jihar, Bayo Lawal ne ya tarbe su a filin jirgin sama na Ibadan, kamar yadda rahotanni suka bayyana, rahoton BluePrint.

Asali: Legit.ng

Online view pixel