Duk Da Rikicin Da Ake Fama Da Shi a Jam'iyyar PDP, Ayu Zai Fice Daga Najeriya

Duk Da Rikicin Da Ake Fama Da Shi a Jam'iyyar PDP, Ayu Zai Fice Daga Najeriya

  • Ana tsaka da rikici a jam'iyyar PDP, Dakta Iyorchia Ayu, ya shirya tafiya zuwa ƙasar wajen na tsawon makonni
  • A wata sanarwa da kakakinsa ya raba wa yan Jarida, Ayu zai kwashe kusan makonni biyu baya ƙasa, ya miƙa mulki ga mataimakinsa
  • A ranar 28 ga watan Satumba, INEC zata ɗage hani kan yakin neman zaɓe ga jam'iyyun siyasa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu, ya shirya fice wa daga ƙasar nan zuwa wata ƙasa da ba'a bayyana ba ranar Laraba mai zuwa.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa duk da ba'a bayyana maƙasudin tafiyar ba, Ayu zai shafe sauran kwanakin da suka rage a watan Satumba a ƙasar waje.

Shugaban PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu.
Duk Da Rikicin Da Ake Fama Da Shi a Jam'iyyar PDP, Ayu Zai Fice Daga Najeriya Hoto: vanguard
Asali: Facebook

A wata sanarwa da mashawarcinsa na musamman kan harkokin sadarwa da kafafen sada zumunta, Simon Imobo-Tswam, ya raba wa manema labarai, Ayu yace zai kwashe "Kusan makonni biyu," a ƙasar waje.

Imobo- Tswana ya bayyana cewa shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, "Zai shilla nahiyar turai Gobe (Laraba)."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Dakta Ayu zai yi fice daga ƙasa na kusan makonni biyu. Yayin da baya nan, mataimakin shugaban jam'iyya (Arewa), Ambasada Iliya Damagun, zai maye gurbinsa."
"Tuni dai shugaban jam'iyya ya sanar da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) matakin miƙa ragamar jagoranci. Ana tsammanin zai dawo gida Najeriya a ƙarshen watan nan."

Za'a fara kamfe a karshen Satumba

INEC ta tsara ɗage haramcin yaƙin neman zaɓe ga jam'iyyun siyasa a ranar 28 ga watan Satumba, 2022 domin fara kamfe gadan-gadan na babban zaɓen 2023.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa nan ba da jimawa ba PDP da sauran jam'iyyu zasu bayyana cikakkun mambobin tawagar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Bayanai sun nuna cewa rashin kawo karshen rikicin gwamna Wike na Ribas da ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, shi ne ya kawo jinkirin rashin bayyana jerin tawagar.

Idan baku manta ba, Ayu, ya wakilta mataimakinsa na yankin arewa ya jagoranci mambobin kwamitin gudanarwa su ziyarci gwamna Wike da sauran fusatattun 'ya'yan PDP da nufin sulhunta rikicin.

A wani labarin kuma Atiku ya bayyana dalilin da yasa suka gaza tunɓuke Shugaban PDP na ƙasa kamar yadda Wike ya nema

Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa a PDP, ta bakin ƙungiyar yaƙin neman zaɓensa yace akwai gagarumar matsala idan aka sauke Ayu.

Kakakin Kamfen ɗin Atiku, Charles Aniagwu, yace PDP ta hango rikicin da ya zarce na yanzu idan ta aiwatar da bukatar Wike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel