Likitoci 38, 000 Sun Bi Bayan Peter Obi, Sun Sha Alwashin Kawo Masa Kuri’u Miliyan 25

Likitoci 38, 000 Sun Bi Bayan Peter Obi, Sun Sha Alwashin Kawo Masa Kuri’u Miliyan 25

  • Wata kungiya mai suna Docs and Medics for Peter Obi ta bulla domin taimakawa takarar Peter Obi a zaben 2023
  • Likitoci da sauran malaman lafiya 38, 000 a karkashin inuwar wannan kungiya za su ba LP kuri’u har miliyan 25
  • Dr. Uche Uzoukwu ya yi bayani ne a hedikwatar jam’iyyar LP, ya fadi dabarar da za su bi domin su cin ma nasara

Abuja - Likitoci akalla 38, 00 da malaman lafiya a asibitoci dabam-dabam sun nuna Peter Obi ne ‘dan takararsu a zaben shugaban kasa na 2023.

Jaridar Sun ta fitar da rahoto cewa dubunnan malaman asibiti za su marawa ‘dan takarar Labour Party baya domin ya karbi shugabancin Najeriya.

Bugu da kari, ma’aikatan lafiyan sun ce za suyi kokari wajen ganin Peter Obi ya samu kuri’a miliyan 25 a zaben da INEC za ta shirya a shekarar badi.

Kara karanta wannan

Wasu Shugabannin PDP na Neman Tada Rikici, Sun ce An Ware Su a Yakin Zaben Atiku

Ta ina kuri’un nan za su fito?

Da yake jawabi a wajen wani taro a hedikwatar Jam’iyyar LP a Abuja, Dr. Uche Uzoukwu ya bayyana yadda za su jawowa Obi kuri’u miliyan 25.

Uche Uzoukwu wanda shi ne shugaban kungiyar Docs and Medics for Peter Obi yace Likitoci da malaman jinya da masu bada magani suna tare da su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Peter Obi
Peter Obi a Jami'ar Columbia University Hoto: @PeterObiGregory
Asali: Facebook

"Likitoci, malaman jinya, da kuma malaman bada magunguna sun shigo karkashin tafiyar ‘Docs and medics for Peter Obi.
Siyasa harka ce ta yawan jama’a, shiyasa kowa yake da muhimmanci. Akwai Likitoci 11, 000 da malaman asibiti 27, 000.
An kafa kungiya a matakin jihohi, muna shiga kananan hukumomi, mun kai matakin mazabu, an nada shugabanni.
Za mu je har rumfunan zabe, za mu samu mutane 500, 000, sai mu karfafa masu wajen kawo mutum 50 a wurin aikinsu

Kara karanta wannan

Tsohon Na Hannun Daman Kwankwaso Ya ki Yarda Ya yi Aiki a Kwamitin Kamfen Peter Obi

A haka za mu iya samun kuri’a miliyan 25. Za mu shirya tarurruka duba marasa lafiya domin ganin Peter Obi ya lashe zabe.”

Ada Orji Nwanyanwu ta bar APGA

Wani labari da zai kara kayatar da magoya bayan Obi shi ne, Ada Orji Nwanyanwu ta sauya-sheka daga APGA zuwa LP, Vanguard ta fitar da rahoton.

Kafin yanzu, Ada Orji Nwanyanwu ce shugabar mata ta jam’iyyar APGA a mataki na kasa. Ita da wasu dinbin ‘ya ‘yan jam’iyyar adawar sun dawo LP.

Shari'ar AA da NNPP

Dazu kun ji labari Jam’iyyar Action Alliance tana karar INEC, NNPP, Rabiu Kwankwaso, da Isaac Idahosa saboda a haramtawa NNPP takara.

Kwatsam sai ga wani Lauya dabam, yace tun tuni kotu ta kori shugabannin jam’iyyar da suka shigar da kara a madadin AA, dole aka daga wannan kara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel