Dino Melaye da Fani-Kayode Sun Dauki Zafi, Sun Yi Wa Junansu Kaca-Kaca a Idon Duniya

Dino Melaye da Fani-Kayode Sun Dauki Zafi, Sun Yi Wa Junansu Kaca-Kaca a Idon Duniya

  • Femi Fani-Kayode ya dauko wata magana da Dino Melaye ya yi a kan zaman Iyorchia Ayu shugaban PDP na kasa
  • Cif Femi Fani-Kayode ya bada shawarar a damke Dino Melaye saboda kalamansa a game da Gwamnonin jihohinsu
  • Wannan ya jawo Sanata Melaye ya maida martani, daga nan sai tsohon Sanatan ya maida masa martani a shafinsa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Dino Melaye wanda ke magana da yawun bakin kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar, ya yi arangama da Femi Fani-Kayode a Twitter.

Legit.ng Hausa ta lura Femi Fani-Kayode ya yi magana a shafinsa na sada zumunta, yana kira ga gwamnatin tarayya da jami’an tsaro su cafke Dino Melaye.

Hakan na zuwa ne bayan an rahoto Sanata Dino Melaye yana mai bayanin yadda gwamnoni suka kashe kudi wajen zaman Iyorchia Ayu shugaban PDP.

Kara karanta wannan

Tsohon Jigon Jam’iyya Ya Fadawa Peter Obi Sirri 5 Na Lashe Zaben Shugaban Kasa

A cewar tsohon Ministan na harkokin jirgin saman, ya kamata ayi ram da Melaye tun da ya tona gwamnonin jihohi da rawar da suka wajen kawo Dr. Ayu.

Baya ga haka Fani-Kayode ya bukaci a hana Atiku Abubakar tsayawa takarar shugaba kasa.

Martanin Sanata Dino Melaye

Amma da Melaye ya tashi maida masa martani, yace ba za a iya fahimtar abin da Fani-Kayode yake nufi ba, yace jagoran na APC ya saba fadan soki-burutsu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dino.
Sanata Dino Melaye da Kashim Shettima Hoto: @dino_melaye
Asali: Facebook

Daily Trust ta rahoto tsohon ‘dan majalisar yace babu dalilin da Femi Fani-Kayode zai kinkimo tsohuwar hirar da aka yi da shi, ya na kafa hujja da ita a yau.

Kakakin na kwamitin yakin neman zaben Atiku yace abin da ya dace shi ne ayi watsi da FFK, amma zai yi karin haske saboda ya warware zare da abawa.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Zargi Gwamnan PDP da Yi wa Duniya Karya Kan Batun Tsaro

Kai kaska ne - FFK ga Dino

Da ya tashi yin raddi a Twitter, Fani-Kayode yace Melaye ba komai ba ne sai kaska a siyasa.

“Me mutum zai ce a game da kaskan da ya bi Nasir El Rufai na shekaru, daga nan ya koma bin Bukola Saraki, sai ya bi Yahaya Bello…
Daga nan ya bi Nyesom Wike, yanzu ya tare a wajen Atiku, ya cigaba da nuna masifar kwadayi."

- Femi Fani-Kayode

Bayan nan tsohon Sanatan na yammacin Kogi ya cigaba da habaici da maganganu a shafinsa na Twitter, har da dauko bidiyo domin cin mutuncin Fani-Kayode.

Wike ya koma Landan

A baya an ji labari Gwamnan jihar Ribas watau Nyesom Wike ya zauna da wasu gwamnoni domin cigaba tattaunawa daga inda aka tsaya a kan rikicin PDP.

Ana tunanin Bola Tinubu zai hadu da Gwamnonin na PDP a kasar waje, wanda hakan barazana ce ga takarar Atiku Abubakar na zama shugaban Najeriya.

Kara karanta wannan

Komawa PDP: Abin da Zan Fadawa Shekarau da Ina Kusa da Shi inji Shugaban NNPP

Asali: Legit.ng

Online view pixel