Shugaba Buhari Ya Zargi Gwamnan PDP da Yi wa Duniya Karya Kan Batun Tsaro

Shugaba Buhari Ya Zargi Gwamnan PDP da Yi wa Duniya Karya Kan Batun Tsaro

  • Samuel Ortom yace jami’an tsaro sun fada masa shugaban kasa ya bada umarnin ka da a taba Makiyaya Fulani
  • Garba Shehu ya maida martani ga Gwamnan na Benuwai, yace idan ya isa ya tona wadanda suka fada masa hakan
  • A cewar Malam Garba Shehu, Gwamna Ortom ya sharara karya ne kurum, kuma hakan zai iya raba kan mutane

Abuja - Fadar shugaban Najeriya ta maidawa Gwamna Samuel Ortom raddi a kan wasu kalamai da ya yi a lokacin da ‘yan jarida suka yi hira da shi.

The Cable ta rahoto cewa Samuel Ortom ya zargi Gwamnatin Muhammadu Buhari da kawo cikas wajen magance matsalar tsaro ta hanyar nuna son kai.

An ji Ortom yana cewa ba don yana girmama tsarin mulkin Najeriya ba, da ya dauki makamai domin tunkarar ‘yan bindigan da suka addabi Najeriya.

Kara karanta wannan

Bidiyon Cikin Katafaren Gidan Matashi Dan Shekaru 15, Ya Ce Mawaki Davido Ba Zai Iya Siyan Irinsa Ba

Mai magana da yawun shugaban kasar yace zargin da Gwamna Ortom yake yi ba gaskiya ba ne, kuma zai jawo rabuwar kai da wadannan kalaman.

Raddin Garba Shehu

“A wata hira da aka yi da shi, Gwamnan Benuwai yayi ikirarin wasu manyan jami’an tsaro sun fada masa Buhari ya ba dakaru umarni su guji taba Makiyaya Fulani.”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

- Garba Shehu

A jawabin da Garba Shehu ya fitar a ranar Laraba, ya kalubalanci Gwamnan ya kama sunayen jami’an tsaron da yake cewa sun fada masa wannan batu.

Shugaba Buhari da Gwamnan Benuwai
Gwamna Ortom a Fadar Shugaban kasa Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC
“Irin wadannan maganganu ba gaskiya ba ne. Idan ya cika namiji kamar yadda yake nunawa, ya fadi sunansu.
Ya kama sunayen wadanda suka fada masa wannan, ko dai ya yi tsit, ka da ya kara magana.”
“Abin takaici ne Ortom da ya bayyana kan shi a matsayin mumuni wanda ya yarda da doka kuma yake girmama tsarin mulki, zai rika karyar da za ta raba kawuna.

Kara karanta wannan

Rashin Tsaro: ‘Yan Gari Sun yi Wa Shugaban Karamar Hukumarsu Ruwan Dutse

'Yan siyasa na kawo sabani

Vanguard ta rahoto Malam Garba Shehu yana cewa a irin lokacin da ake fama da matsalar tsaro, kamata yi ‘yan siyasa su dage wajen hada-kan al’umma.

A madadin haka, hadimin shugaban kasar ya zargi Ortom da jefa gabar kabilanci da sabanin addini

A karshe, Shehu yake cewa kowa ya san irin wadannan labaran soki-burutsu na Gwamna Ortom sam ba gaskiya ba ne, kuma ba a kan shi aka fara ba.

Ci da addinin Peter Obi

Dazu kun ji labari Ifeanyi Arthur Okowa ya zargi ‘Dan takaran shugaban kasa na jam’iyyar Labor Party watau Peter Obi da kokarin ci da addini a 2023.

A manyan ‘yan takaran shugaban kasa da ake da su, Peter Obi ne kurum kirista, don haka yake samun damar zama da kiristoci a coci domin jawo ra’ayinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel