Sulhu a Jam’iyyar PDP Ya Gagara, Wike da Gwamnoni Sun Yi Kus-Kus a Landan

Sulhu a Jam’iyyar PDP Ya Gagara, Wike da Gwamnoni Sun Yi Kus-Kus a Landan

  • Gwamna Nyesom Wike ya yi zama da su Gwamna Seyi Makinde da Gwamna Samuel Ortom a birnin Landan
  • Nyesom Wike da Samuel Ortom ne suka tashi daga Najeriya, suka zauna da Seyi Makinde wanda yana Ingila
  • Bisa dukkan alamu jam’iyyar PDP ta gaza sasanta Gwamnan jihar Ribas da ‘dan takaranta, Atiku Abubakar

UK - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike da kuma takwarorinsa na jihohin Oyo da Benuwai, Seyi Makinde da Samuel Ortom sun hadu a Landan.

Vanguard ta fitar da rahoto dazu, ta tabbatar da cewa wadannan gwamnonin jihohin na PDP sun yi zama ne a ranar Juma’a, 2 ga watan Satumba 2022.

Wani na kusa da gwamnonin ya shaidawa manema labarai cewa Gwamnan Oyo, Seyi Makinde yana Ingila tun tuni, inda yake hutunsa na shekara.

Nyesom Wike da Samuel Ortom ne suka biya Landan domin haduwa da Makinde, ana zargin sun tattauna game da matsayar da za su dauka a PDP.

Kara karanta wannan

Shugabannin PDP 3 da Aka Yi da Gwamna Wike Ya yi Rigima Da Su a Jere

Gwamnonin biyu sun fito daga Najeriya, suna kan hanyar zuwa Amurka, sai suka yada zango a Ingila, Makinde ya kwana biyu yana kasar Turan.

Babu sulhu da Atiku a PDP

Kamar yadda wani babba a PDP yake fada, idan dai ba wani ikon Ubangiji ba, maganar sulhu tsakanin Atiku Abubakar da Nyesom Wike ta wargaje.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamnan Ribas
Gwamna Nyesom Wike Hoto: @GovWike
Asali: Facebook

A cewar wannan jami’i na jam’iyyar adawar, ‘dan takaran shugaban kasa a APC, Asiwaju Ahmed Tinubu, zai sake yin zama da wadannan gwamonin.

Atiku yana ruwa kenan?

A taron da za suyi ne ake sa ran cewa gwamnonin za su karkare maganar da suka fara da Bola Tinubu. Wannan yunkuri zai kawowa PDP cikas a 2023.

Daily Post a rahoton da ta fitar, ta bayyana cewa ‘yan bangaren Wike sun sha alwashin taimakawa sauran jam’iyyu wajen dankara su Atiku Abubakar da kasa.

Kara karanta wannan

Zulum Ya Kayar Da Wike Da Sauran Takwarorinsa, An Alantashi Matsayin Gwarzon Gwamnan Shekara

Wata majiyar tace Gwamna Wike da mutanen da ke tare da shi ba su da niyyar barin jam’iyyar PDP, za su zauna domin ganin abin da zai biyo bayan zabe.

Wike a rigingimun PDP

Kun ji labari tsakanin shekarar 2016 zuwa 2022, Jam’iyyar PDP tayi shugabanni na kasa hudu, sai da Nyesom Wike ya yi rigima da uku daga cikinsu.

An samu sabani tsakanin Gwamnan da Ali Modu Sheriff, sannan ya juyawa Uche Secondus baya a 2021, kuma yau babu jituwa da shi da Iyorchia Ayu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel