Gwamnan PDP Ya Halarci Gangamin Taron Peter Obi, Hadiminsa Ya Fadi Gaskiya

Gwamnan PDP Ya Halarci Gangamin Taron Peter Obi, Hadiminsa Ya Fadi Gaskiya

  • Gwamnan jihar Oyo ya musanta jita-jitar da ake yaɗa wa cewa ya halarci gangamin taron magoya bayan Obi a Ibadan
  • Sakataren watsa labarai na gwamna Makinde ya ce labarin karya ce da aka shirya da nufin gurbata tunanin mutane
  • Gwamnan na jam'iyyar PDP ba ya cikin jihar lokacin da taron ya gudana ranar 3 ga watan Satumba, 2022

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Oyo - Sakataren watsa labarai na gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo, Taiwo Adisa, yace Mai gidansa bai halarci gangamin taron jam'iyyar LP da aka shirya domin girmama Peter Obi a birnin Ibadan ba.

Punch tace Adisa ya ayyana rahoton da ake yaɗa wa cewa gwamnan ya ƙara haskaka gangamin da, "Ƙagaggiyar ƙaryya da aka kirkiro domin jefa ruɗani a zaukatan mutane."

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde.
Gwamnan PDP Ya Halarci Gangamin Taron Peter Obi, Hadiminsa Ya Fadi Gaskiya Hoto: punchng.com
Asali: UGC

A wata sanarwa da Hadimin gwamnan ya fitar ranar Asabar, yace Makinde, wanda ya ɗauki hutu bayan ya damƙa ragamar mulki hannun mataimakinsa, Bayo Lawal, har yanzu bai dawo Ibadan ba.

Kara karanta wannan

2023: Bola Tinubu Ya Magantu Kan Rikicin Atiku da Wike, Ya Raɗa Wa PDP Sabon Suna

A cewarsa, gwamna bai koma birnin Ibadan ba lokacin da aka gudanar da Gangamin magoya bayan Obi "Obidient" wanda aka yaɗa farfagandar ya halarta, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani sashin sanarwan yace:

"An jawo hankalin mu kan wani labari da ake yaɗa wa a Intanet, wanda ya nuna cewa an hangi Makinde a wurin gangamin taron Obidient wanda ya gudana a Ibadan, ranar Asabar 3 ga watan Satumba, 2022."
"Ba tare da dogon zance ba labarin ƙarya ce da aka lullube da nufin yaudara. Don share tantama gwamna Makinde ba ya kusa da Ibadan lokacin da taron ya gudana. Ta ya wanda ya tafi hutu waje za'a gan shi wurin gangami?"
"Yayin da ba zamu iya dakile Farfagantar da magoya bayan Obi suka kudirin aniyar yaɗawa kan ɗan takarar su ba, ba zamu zuba ido muna kallo ana shirin taɓa ƙimar gwamna ta hanyar masa ƙarerayi ba."

Kara karanta wannan

2023: Wani Babban Jigon APC da Dubbannin Magoya Baya Sun Sauya Sheka Zuwa PDP

Gwamna Makinde bai halarci taro da Atiku ba

A wani labarin kuma Lamari Ya Caɓe, An Nemi Mutum Uku An Rasa a Wurin Taron Atiku da Yan Takarar PDP Na 2023

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya gana da yan takarar gwamnonin jihohi a inuwar PDP a Abuja.

Sai dai taron ya kara haska ɓarakar PDP domin ba'a hangi yan takara daga jihohin Ribas da Abiya ba da kuma gwamnan Oyo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel