Gaskiyar Abinda Ya Faru Game Da Ruwan Jifan Da Aka Yiwa Kwankwaso A Jihar Kogi

Gaskiyar Abinda Ya Faru Game Da Ruwan Jifan Da Aka Yiwa Kwankwaso A Jihar Kogi

  • Kungiyar yakin neman zaben shugabancin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ta ce babu wanda ya jefi tawagarsa a jihar Kogi
  • Kakakin kungiyar, Ladipo Johnson, ya ce Kwankwaso ya samu kyakkyawar tarba a wajen al'ummar Kogi masu kirki tun daga shigarsa jihar
  • Jam'iyyar ta NNPP ta ce za su dauki mataki kan wadanda suka yada wannan labarin kanzon kuregen

Kogi - Kungiyar yakin neman zaben Rabiu Musa Kwankwaso ta yi watsi da rahoton cewa yan iskan gari sun jefi dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) a jihar Kogi.

Mun ji a baya cewa wasu da ake zargin yan jagaliya ne sun jefi Kwankwaso da ledojin ruwa yayin da ya kai ziyara jihar.

Kwankwaso da jama'a
Gaskiyar Abinda Ya Faru Game Da Ruwan Jifan Da Aka Yiwa Kwankwaso A Jihar Kogi Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Twitter

Kwankwaso dai ya je Lokoja, babban birnin jihar ta Kogi don kaddamar da sakatariyar jam’iyyar da ofishoshin kamfen dinsa.

Kara karanta wannan

Yadda ‘Yan Iskan Gari Suka Wulakanta ‘Dan takaran NNPP, Kwankwaso a Kogi

Amma da take martani ga rahoton a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun kakakinta, Ladipo Johnson, kungiyar kamfen din ta tabbatar da cewar dan takarar shugaban kasar ya samu kyakkyawar tarba cike da soyayya a Kogi, jaridar Punch ta rahoto.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jawabin ya ce:

“An ja hankalinmu zuwa ga wasu rahotannin kafofin watsa labarai, wanda ke hasashen cewa an farmaki ayarin motocin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria People’s Party a jihar Kogi.
“Da isarsa jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya samu kyakkyawar tarba cike da kauna daga mutanen jihar Kogi masu kirki. A ranar Larabas, ya ziyarci iyalan amininsa, tsohon gwamnan jihar Kogi, Marigayi Prince Abdullahi Audu a mahaifarsa. Daga nan, ya garzaya cibiyar taro ta garin Lokoja don kaddamar da sabuwar hedkwatar jam’iyyarsa ta jiha.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Mai Magana da Yawun Rundunar 'Yan Sanda a Najeriya Ya Mutu

“Muna masu son bayyana cewa ciki da tsakanin wadannan wurare biyu, babu inda aka jefi ayarin motocin dan takarar shugaban kasar ko kuma ya samu tarba mara dadi daga mutanen jihar Kogi masu kirki.
“Bugu da kari, sabanin rahotannin kafofin watsa labarai, muna son tabbatar da cewar babu wani mutum nai suna “Musa Yunusa” a tawagar Kwankwaso. Don haka, kakafen watsa labarai ba za su iya dogaro kan sunan wani fatalwa ba don kirkirar lamarin da bai ma faru bat un da farko.
“Kungiyar kamfen din Kwankwaso na neman hanyoyin da ya dace don tabbatar da ganin cewa an hukunta wadanda suka watsa wannan labaran karyan.
“Muna kuma umurtansu da su tabbatar da kowani labara da ya danganci Mai girma Rabiu Musa Kwankwaso, ta masu magana yawunsa. Sannan su kuma janye daga batar da jama’a musamman a irin wannan lokacin.”

2023: Za A Gwabza Zabe Mai wahalan Da Ba A Taba Yin Irinsa Ba A Tarihin Najeriya, Inji APC

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Zulum Ya Ci Taliyar Ƙarshe, NNPP Za Ta Ƙwace Borno A 2023

A wani labarin, jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta bayyana cewa babban zaben 2023 zai zamo mafi wahala tun bayan samun yancin kan Najeriya a 1960, Daily Trust ta rahoto.

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu ne ya bayyana hakan a yayin taron yiwa Najeriya da takarar Tinubu/Shettima addu’a wanda kungiyar mata ta WIFE ta shirya a ranar Alhamis, 1 ga watan Satumba, a Abuja.

Adamu, wanda ya samu wakilcin mataimakiyar shugabar matan APC na kasa, Hajiya Zainab Ibrahim, ya ce zaben zai fi kowanne wahala ne saboda zai kasance “kimiyya tsanta.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel