Kashim Shettima Ya Shawo Kan ‘Dan Majalisar Daura, Ya Fasa Barin Jam’iyyar APC

Kashim Shettima Ya Shawo Kan ‘Dan Majalisar Daura, Ya Fasa Barin Jam’iyyar APC

  • Babu mamaki Fatuhu Muhammad ya canza shawarar da ya yanke a baya na sauya-shekarsa daga jam’iyyar APC mai mulki
  • Sanata Kashim Shettima yace Hon. Fatuhu Muhammad ya fasa ficewa daga APC a sakamakon wata tattaunawa da aka yi da shi
  • Kashim Shettima ya hadu da ‘dan majalisar na Daura/Sandamu/Mai’adua tare da Hon. Salisu Sani Zango da Rt. Hon. Idris Wase

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Sanata Kashim Shettima yana cigaba da kokarin dinke kan ‘ya ‘yan jam’iyyar APC, hakan ta kai ya yi zama da Honarabul Fatuhu Muhammed.

Kafin yanzu Fatuhu Muhammed ya bada sanarwar barin jam’iyyar APC mai mulki. Kashim Shettima yace ‘dan majalisar ya canza shawara yanzu.

Da yake bayani a shafin Facebook, ‘dan takaran mataimakin shugaban kasar na APC ya tabbatar da cewa ya yi zama da Muhammad a yammacin jiya.

Maganar Kashim Shettima

“A yunkurinmu na dinke baraka da hada-kan ‘ya ‘yan jam’iyyarmu ta APC, nayi zama da Honarabul Fatuhu Muhammed, wanda a baya ya bada sanarwar barin jam’iyyarmu.
Fatuhu Muhammed mai wakiltar mazabar Daura/Sandamu/Mai’adua, jigo ne a APC a Katsina.”

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Bayan muhimmiyar tattaunawa da yammacin nan (Litinin), Hon. Fatahu ya janye matakin da ya dauka a baya na sauya-sheka, ya jaddada niyyarsa na yi mana aiki, musamman a zaben 2023.”

- Kashim Shettima

‘Dan Majalisar Daura
Fatuhu Muhammad tare da su Sanata Kashim Shettima Hoto: kashimshettima.org
Asali: Facebook

'Yan tawagar sasanta rigimar gida

Katsina Post ta kawo rahoton, tace wadanda aka yi zaman da su sun hada da mataimakin shugaban majalisar wakilai, Rt. Hon. Ahmed Idris Wase.

Shettima yace Hon. Nasiru Sani Zangon Daura ya samu halartar wannan zaman sulhu.

Nasiru Sani Zangon Daura shi ne ‘dan majalisar mazabun Zango/Baure mai-ci, kuma ‘dan takaran APC na kujerar Sanatan Arewacin jihar Katsina a 2023.

Ana shawo kan 'ya 'yan jam'iyya

Kafin yanzu Kashim Shettima ya yi zama da tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina, Mustapha Muhammad Inuwa wanda ya rasa tikitin gwamna.

Legit.ng Hausa ta fahimci jagororin na APC suna bin ‘ya ‘yan jam’iyyar irinsu Mustapha Inuwa domin su hana su tsallakawa jam’iyyar hamayya.

Atiku zai hade da Obi?

A rahoton da muka fitar, an ji maganar cewa Alhaji Atiku Abubakar ya sa labule da Peter Obi a kasar waje ba gaskiya ba ne inji Kwamitin yakin zaben Obi.

Kwamitin na yakin takara ya zargi masu neman kashewa Peter Obi kasuwa da yada jita-jitar cewa ‘dan takaransu zai bi bayan jam’iyyar PDP a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel