2023: Da Yawa Cikin 'Yan Takarar Shugabancin Kasa Yashe Najeriya Suke da Buri, Wike

2023: Da Yawa Cikin 'Yan Takarar Shugabancin Kasa Yashe Najeriya Suke da Buri, Wike

  • Gwamna Wike na jihar Ribas ya fallasa cewa, da yawan 'yan takarar shugaban kasa a 2023 handame kudin baitul malin Najeriya suke son yi
  • Ya sanar da cewa, duk masu ihun zasu ceto Najeriya da 'yan Najeriya suna da burinsu na kansu kuma zai fallasa su idan lokaci yayi ta yadda za a gane su
  • Wike ya sanar da cewa, a rigimar da ake ta jam'iyyar PDP ba a yi komai ba, amma nan gaba kadan wani abu zai faru

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Ezenwo Wike, yace da yawa daga cikin 'yan takarar shugabancin kasa dake hararo kujerar shugaban kasa a 2023 ba su yi wa Najeriya fatan alheri saboda baitul malin kasar suke hangowa.

Kamar yadda jaridar Leadership ta rahoto, yace yana matsayin da zai fi sanin hakan kuma yace zai bayyana wadannan 'yan takarar a lokacin da ya dace ta yadda 'yan Najeriya zasu yi amfani da kuri'unsu don kayar da su.

Nyesom Wike
2023: Da Yawa Cikin 'Yan Takarar Shugabancin Kasa Yashe Najeriya Suke da Buri, Wike. Hoto daga leadership.ng
Asali: UGC

Wike ya sanar da hakan a ranar Litinin yayin kaddamar da ayyukan titi da aka yi a Rumuesara, garin Eneka dake karamar hukumar Obi/Akpor dake jihar Ribas.

Gwamnan yace:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Wasu mutane suna can suna fama da yadda zasu karba shugabancin Najeriya domin su kwashe ragowar da mutanen nan suka bari.
“Na samu damar sani kuma lokaci nake jira wanda ya dace zan sanar da ku su waye mutanen nan. Akwai bukatar ku san abinda ke faruwa a Najeriya. Ku manta da wadannan dake yawo hankali tashe suna cewa zasu ceto ku ko Najeriya. Ku zuba ido ku ga abinda zai faru.

"Dukkanmu mu kwantar da hankalinmu a kan abinda ke faruwa a PDP. A takaice babu abinda ya faru. Amma da izinin Ubangiji wani abu ya kusa faruwa."

Daura ta Cika ta Batse da Jiga-Jigan 'Yan Siyasa da Boko Yayin da Tsohon DG DSS ke Aurar da Diya

A wani labari na daban, Daura, garinsu shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cika ya batse yayin da tsohon darakta janar na hukumar tsaron farin kaya, DSS, Alhaji Lawal Musa Daura, ya aurar da diyarsa.

Lawal ya aurar da kyakyawar diyarsa ga masoyinta, haifaffen garin Gusau, Injiniya Abdullahi Lawal Abba a garin Daura a ranar Juma'a, Daily Trust ta rahoto.

Babban Limami Sheikh Abdulkadir Ibrahim ne ya daura auren da aka yi a masallacin Low Cost dake Daura.

Asali: Legit.ng

Online view pixel