Kwamitin Gudanarwar Uwar Jam'iyyar PDP Ta Shiga Ganawar Sirri da Yan Takara

Kwamitin Gudanarwar Uwar Jam'iyyar PDP Ta Shiga Ganawar Sirri da Yan Takara

  • Uwar Jam'iyyar PDP ta tattara yan takararta a birnin tarayya Abuja don tattaunawa da su
  • Jam'iyyar adawa ta PDP na shirye-shiryen fuskantar zaben 2023 da zai gudana a watan Febrairu
  • Har Ila Yau ana cigaba da zaman sulhu tsakanin dan takarar shugaban kasa jam'iyyar Atiku Abubakar da Nyesom Wike

Abuja - Kwamitin Gudanarwar Uwar Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta shiga ganawar sirri da yan takarar gwamna karkashin tutarta a fadin jihohin Najeriya 36.

Dukkan yan takarar kujeran gwamna na PDP ke hallare a zaman illa gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde da na Bauchi, Bala Mohammed AbdulKadir, rahoton Leadership.

Yayin Bala Abdulkadir ya bada hakurin cewa yana kan hanya, Seyi Makinde na birnin Landan inda suka je ganawa da dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Hantar Atiku da PDP Ta Kada Bayan Samun Bayanin Zaman Tinubu da Wike a Landan

An yiwa zaman take taron tattaunawa tsakanin shugabannin uwar jam'iyya da yan takara a zaben 2023.

Wannan ganawa na zuwa ne daidai lokacin da ake kira ga Shugaban uwar jam'iyyar, Iyorchia Ayu, yayi murabus bisa sharadin da Wike da mabiyansa suka gindayawa PDP don sulhu tsakaninsa da Atiku.

Wadata
Kwamitin Gudanarwar Uwar Jam'iyyar PDP Ta Shiga Ganawar Sirri da Yan Takara
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A Rabu Da Wike, Yayi Duk Abinda Ya Ga Dama: Sule Lamido

A wani labarin kuwa, tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya ce babu wani laifi da aka yiwa Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike kuma a rabu da shi yayi abinda ya ga dama.

Lamido ya bayyana hakan ne a hirar da yayi a shirin Politics Today na tashar Channels TV

Yace jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP na da kundin tsarin mulki da dokoki kuma zabe akeyi don zaben duk wani dan takara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel