2023: Tsohon ‘Dan adawan Buhari da APC Ya Fadi Dalilin Komawa Bayan Tinubu

2023: Tsohon ‘Dan adawan Buhari da APC Ya Fadi Dalilin Komawa Bayan Tinubu

  • Jigo yanzu a jam’iyyar APC, Femi Fani-Kayode ya fito gadan-gadan yana goyon bayan Bola Tinubu a babban zaben shekarar badi
  • Shekarun baya kadan, Cif Fani-Kayode yana cikin wadanda suka fi kowa ragargazar gwamnatin Muhammadu Buhari da APC
  • Tsohon Ministan ya fi tsoron mulki ya zauna a Arewa a a kan Musulmai su yi takarar shugaban kasa da mataimaki a Najeriya

Abuja - Tsohon Ministan tarayya, Femi Fani-Kayode, ya yi bayanin abin da ya sa yake goyon bayan ‘dan takaran APC a zaben 2023, Asiwaju Bola Tinubu.

Da aka tattauna da shi a gidan talabijin Channels, Femi Fani-Kayode ya ce saboda rajin kansa da neman hadin-kan kasa yake goyon-bayan Bola Tinubu.

'Dan siyasar yake cewa ra’ayinsa bai da alaka da daidai ko akasin haka, illa iyaka ya dauki zabi a matsayinsa na daya daga cikin ‘ya ‘yan jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

2023: Fani-Kayode Ya Gana Da Tinubu A Abuja, Ya Aika Wa PDP Sako Mai Karfi

Fani-Kayode ya fake da cewa zaman Najeriya kasa guda yana fuskantar barazana idan har aka goyi bayan wani ‘Dan Arewa ya sake karbar shugabanci a 2023.

“Maganar zabi ne. A lokacin da nake PDP, na yaki wadanda suke adawa da jam’iyyata. Yanzu da ba na PDP, ina APC, zan yaki masu fada da jam’iyyata.

- Femi Fani-Kayode

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wannan ne hali na, kuma ina daukar zabi ne la’akari da abin da na natsu da shi da kuma jajircewa.

Fani Kayode
Femi Fani Kayode Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Mulki ba zai koma Kudu ba

Muhimmin abu shi ne barazana ga hadin-kan Najeriya ta yadda mulki ba zai koma Kudu ba, bayan Hausa/Fulani sun yi shekaru takwasu su na shugabanci.

A baya, Cif Fani-Kayode yana cikin manyan masu sukar shugaba Muhammadu Buhari, yana zargin gwamnatinsa da yunkurin musuluntar da Najeriya.

Vanguard tace wannan karo, jigon na APC bai ga laifin a tsaida Musulmi-Musulmi a matsayin takarar shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa ba.

Kara karanta wannan

Ana Za a Bar Mulki, Tsohon ‘Dan Majalisa yace Ganduje Bai Ci Zaben 2019 ba

A yanzu da ya shiga jam’iyya mai mulki, ya daina adawa, Fani-Koyode yace yadda yake kallon abubuwa ya canza musamman da Tinubu ya samu takara.

Tafiyar Kashim Shettima da Tinubu

Rahoton yace tsohon jigon na PDP ya wanke Kashim Shettima daga masu korafi, yace a lokacin Shettima yana Gwamna, ya fi kowa gina coci a Najeriya.

“Hakika akwai matsala tattare da tikitin Musulmi-Musulmi, Akwai matsala da wannan, duk Kiristan da ya fada maka yana farin ciki, ba na kwarai ba ne.”

- Femi Fani-Kayode

Baki yake yanka

Kun ji labarin yadda baki yake yanka wuya domin an tunawa Shugaban PDP abin da ya fada a gaban Duniya da ya karbi shugabancin Jam’iyyar a 2021.

Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa da bangaren Nyesom Wike sun ce dole ne a tunbuke Iyorchia Ayu tun da 'dan Arewa aka ba tikiti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel