2023: Jagoran APC, Bola Tinubu, Zai Gana da Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo Yau

2023: Jagoran APC, Bola Tinubu, Zai Gana da Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo Yau

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu, ya shirya gana wa da Obaasanjo yau a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun
  • Bayanai sun nuna cewa jim kaɗan bayan tattaunawarsa da tsohon shugaban, Tinubu zai yi jawabi ga mutane a filin MKO Abiola
  • Wannan shi ne karo na uku da tsohon gwamnan Legas ke kai ziyara Ogun a shirinsa na gaje Buhari a 2023

Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa karkaashin inuwar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, zai gana da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, yau Laraba a Abeokuta, jihar Ondo.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa taron wani ɓangare ne na ziyarar neman shawari da ɗan takarar ke yi domin cimma burinsa na zaman shugaban kasa a 2023.

Bola Tinubu da Obasanjo.
2023: Jagoran APC, Bola Tinubu, Zai Gana da Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo Yau Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Sakataren watsa labarai na gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun, Kunle Somorin, shi ne ya bayyana haka yau Laraba da safe.

Kara karanta wannan

Zan Yanke Hukunci Kan Ko Zan Fice Daga Jam'iyyar Kwankwaso A Wannan Makon, Shekarau Ya Magantu

A rahoton Leadership, Somorin ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Mun fahimci cewa ɗan takarar shugaban ƙasa karkashin APC, Asiwaju Bola Tinubu, zai kawo ziyara Abeokuta, jihar Ogun, yau Laraba, 17 ga watan Agusta, 2022."
"Ya tsara zai sa labule da tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, da misalin ƙarfe 10:00 na safe sannan ya yi jawabi ga mutane a filin ƙasa-da-ƙasa MKO Abiola jim kaɗan bayan kammala wa."

APC ta tabbatar da ziyarar

A wata sanarwar ta daban da shugaban APC reshen Ogun, Yemi Sanusi, ya fitar ya ce, "Baki ɗaya mambobin kwamitin gudanarwa da shugaban jam'iyya na jiha zasu halarta."

"Asiwaju zai shigo Ogun: Muna sanar da cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu, zai kawo ziyara Abeokuta, jihar Ogun, yau Laraba. Dukkan shugabanni da shugaban jam'iyya su halarta da wuri ƙarfe 10:00 na safe."

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ne Zai Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa a 2023, Tsohon Makusancin Buhari

Legit.ng Hausa ta gano cewa wannan shi ne karo na uku da tsohon gwamnan zai kai zuyara Ogun kan burinsa na zama shugaban ƙasa.

A wani labarin kuma Yan majalisu biyu da dubbannin yan siyasa sun sauya sheka zuwa PDP a gangamin Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya karbi dubbannin mambobin jam'iyyu da suka koma PDP a Adamawa.

Atiku Ya kai ziyara mahaifarsa a karon farko tun bayan lashe tikitin takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262