2023: Kwankwaso Ne Shugaban Ƙasa Na Gaba A Najeriya, Buba Galadima

2023: Kwankwaso Ne Shugaban Ƙasa Na Gaba A Najeriya, Buba Galadima

  • Buba Galadima, babban jigon jam'iyya mai kayan marmari ya yi hasashen Kwankwaso zai lashe zaɓen shugaban kasa a 2023
  • Tsohon makusancin shugaba Buhari ya bayyana yadda tsohon gwamnan Kano zai yi nasara a jihohin ƙasar nan
  • Jam'iyyar NNPP ta tsayar da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso takarar shugaban ƙasa ba tare da hamayya ba a zaben fidda gwani

Abuja - Jigo a jam’iyya mai kayan marmari NNPP, Buba Galadima, ya yi ikirarin cewa dan takarar shugaban kasa, Rabi’u Musa Kwankwaso, ne zai gaji shugaban kasa, Muhammadu Buhari a 2023.

Daily Trust ta rahoto Galadima na cewa Kwankwaso zai yi nasara a baki ɗaya jihohin arewa maso yamma kana ya samu kuri’u isassu a sauran shiyyoyin Najeriya a zaben shugaban kasa da ke tafe a 2023.

Buba Galadima.
2023: Kwankwaso Ne Shugaban Ƙasa Na Gaba A Najeriya, Buba Galadima Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Galadima, wanda tsohon makusancin Buhari ne, ya yi wannan furucin ne a wata hira da Arise TV kan lamurran da suka shafi siyasar Najeriya.

Kara karanta wannan

Yan Majalisu Biyu Da Dubbannin Yan Siyasa Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a Gangamin Atiku

A cewarsa, shiyyar arewa maso yamma da ke da masu katin zabe miliyan 24m, baki ɗayansu zasu dangwala wa zaki ne watau Kwankwaso shi ɗaya tilo a 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A jawabinsa, Galadima ya ce:

“Ya kamata ƴan Najeriya su san abin da ke tunkaro su, mu ɗauki arewa maso gabas inda ni kaina na fito, Kwankwaso zai yi nasara jihohin Bauchi, Gombe, Adamawa, da Taraba. Jihohin da za'a kai ruwa rana da APC ba su wuce Borno da Yobe ba."
“Idan muka koma arewa ta tsakiya, za lashe jihohin Filato da Nasarawa, a fasahance zamu yi nasara Benue, bare kuma Kogi da take gidansa na biyu.Haka zamu lashe jihar Neja, Kwara ta dawo hannun mu daga kai ziyara."
“Jihar Kuros Riba, Akwa Ibom, Edo, da Oyo duk suna cikin lissafin inda zamu lashe. Muna faɗi tashin kwace Delta, idan ta shigo cikin jihohin da zai samu kuri'u mafi rijaye, to Kwankeaso ne zai zama a sahun farko, ya ɗare shugaban Najeriya.”

Kara karanta wannan

‘Yan Majalisar Dattawa Sun yi Magana a kan Yunkurin Radawa Kaduna Sabon Suna

Bugu da ƙari, Buba Galadima, ya ce ko da yan Najeriya sun buga siyasar ƙabilaci da addini ne a zaɓe mai zuwa, Kwankwaso ne zai lashe zaɓen.

Atiku a Adamawa

A wani labarin kuma Yan Majalisu Biyu Da Dubbannin Yan Siyasa Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a Gangamin Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya karbi dubbannin mambobin jam'iyyu da suka koma PDP a Adamawa.

Atiku Ya kai ziyara mahaifarsa a karon farko tun bayan lashe tikitin takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel