Tsohon Gwamna Dariye Ya Musanta Shirin Tsayawa Takarar Sanatan Filato

Tsohon Gwamna Dariye Ya Musanta Shirin Tsayawa Takarar Sanatan Filato

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yiwa wasu da aka daure bisa sace kudin afuwa, 'yan Najeriya sun fusata
  • A makon nan ne aka samu rahotannin da ke cewa, tsohon gwamnan Filato Dariye zai tsaya takarar sanata
  • A rahoton da muka samo yau Juma'a, tsohon gwamnan ya musanta aniyar tsayawa takara tare da yin karin haske

Jihar Filato - Tsohon gwamnan jihar Filato, Joshua Dariye, wanda aka saka kwanan nan daga gidan yari watanni uku bayan da Buhari ya yi masa afuwa, ya ce ba zai wani tsaya takarar kujerar majalisar dattawa ta Filato ta tsakiya ba a zaben 2023 ba.

Dariye, wanda ke zaman gidan yari na shekaru 10 a gidan yari, ya shaki iskar 'yanci a ranar Litinin din da ta gabata bayan kimanin shekaru hudu yana daure.

Kara karanta wannan

Buhari: Da zarar an yi kidaya a 2023, za a samu mafita ga matsalar rashin tsaro

Tun bayan da aka sake shi ake ta ta rade-radin cewa tsohon gwamnan ya kammala shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar Labour, domin karbar fom din takarar sanata domin wakiltar al’ummar yankin Filato ta tsakiya.

Ba zan tsaya takarar sanata ba, inji Dariye
Dariye Ya Musanta Shirin Tsayawa Takarar Sanatan Filato | Hoto: pulse.ng
Asali: UGC

Sai dai da yake magana a wani taro, Dariye ya yi watsi da hakan, inda ya karya ajita-jitar aniyarsa ta tsayawa takarar Sanata, kuma ya ce ba shi da niyyar tsayawa takarar a 2023 ko da wasa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya bayyana hakan ne a lokacin da gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, ya jagoranci tawagar jihar da suka ziyarci Dariye da tsohon gwamnan jihar Taraba, Rabaran Jolly Nyame, domin taya su murna samun 'yanci da kuma afuwar Buhari.

Batun gaskiya game da takarar Dariye

Sanarwar da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Lalong, Macham Makut ya fitar a ranar Juma’a bayan ziyarar ta ce:

Kara karanta wannan

Daga Fitowa daga Kurkuku, Dariye Zai Shiga Takara, Ana Masa Harin Kujerar Sanata

“Shi (Dariye) ya ba da labarin irin wahalar da ya sha a gidan yari, ya ce lokaci ne mai wahala amma Allah ya taimake shi kuma ya sa ya tsira.
“Dariye ya kuma karyata rade-radin da ake yadawa na cewa ya fito takarar Sanata, yana mai bayyana hakan a matsayin batu mara tushe kuma ba gaskiya ba ne domin bai sayi fom ba ko kuma ya yi wani abu mai kama da haka."

Hakazalika, sanarwar ta bayyana cewa nan da mako mai zuwa ne Dariye zai je Jos domin gode wa magoya bayansa da masoya da suka tsaya masa a tsawon wadannan shekaru, kamar yadda Pulse ta ruwaito.

Daga Fitowa daga Kurkuku, Dariye Zai Shiga Takara, Ana Masa Harin Kujerar Sanata

A wani labarin, idan abubuwa sun tafi yadda ake so, Joshua Dariye zai bayyana niyyarsa na yin takarar Sanata mai wakiltar Filato ta tsakiya a zaben 2023.

Kara karanta wannan

2023: Babangida Aliyu Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Atiku Zai Ci Jihar Rivers Da Sauran Jihohin Kudu Maso Kudu

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto dazu cewa Joshua Dariye zai nemi kujerar ‘Dan majalisar dattawa a karkashin jam’iyyar hamayya ta Labor Party.

Tsohon gwamnan zai nemi ya sake wakiltar mutanen yankin Filato ta tsakiya a majalisa. Sanata Dariye wanda ya shafe kusan shekaru hudu a daure a gidan kurkuku zai koma siyasa, ya sake jarraba farin jininsa a zabe mai zuwa na 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel