Daga Fitowa daga Kurkuku, Dariye Zai Shiga Takara, Ana Masa Harin Kujerar Sanata

Daga Fitowa daga Kurkuku, Dariye Zai Shiga Takara, Ana Masa Harin Kujerar Sanata

  • Babu mamaki Joshua Dariye ya sake zama ‘Dan Majalisar Dattawan Najeriya a 2023
  • Ana shirin ba tsohon Gwamnan tutar neman takara a karkashin jam’iyyar LP a Filato
  • Kwanan nan ‘Dan siyasar ya fito daga gidan gyaran hali, an yafe masa laifin satar N1.12bn

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Plateau - Idan abubuwa sun tafi yadda ake so, Joshua Dariye zai bayyana niyyarsa na yin takarar Sanata mai wakiltar Filato ta tsakiya a zaben 2023.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto dazu cewa Joshua Dariye zai nemi kujerar ‘Dan majalisar dattawa a karkashin jam’iyyar hamayya ta Labor Party.

Tsohon gwamnan zai nemi ya sake wakiltar mutanen yankin Filato ta tsakiya a majalisa.

Sanata Dariye wanda ya shafe kusan shekaru hudu a daure a gidan kurkuku zai koma siyasa, ya sake jarraba farin jininsa a zabe mai zuwa na 2023.

Kara karanta wannan

'Yancin 'yan Najeriya ne: Jigon Amurka ya ce 'yan majalisa ba su da 'yancin tsige Buhari

LP za ta kuma karbar Dariye

Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa jam’iyyar Labor Party ta reshen jihar Filato ta shirya domin karbar tsohon Gwamnan a Filato, a yanzu yana Abuja.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

‘Dan siyasar ba bako ba ne a jam’iyyar hamayyar, domin bayan ya yi gwamna na shekaru takwas a Filato, ya sauya-sheka daga PDP zuwa LP a 2011.

Majalisar Dattawa
Sanatoci a Majalisar Dattawa Hoto: @NgrSenate
Asali: UGC

A karkashin jam’iyyar LP ne Dariye ya yi takara, kuma ya zama ‘Dan majalisar dattawan Najeriya. A 2015 ya samu damar zarcewa a kan kujerarsa.

Da aka zanta da wani shugaba a jam’iyyar ta LP a Filato, ya tabbatar da cewa babu shakka za su ba tsohon gwamnan tikitin yin takarar ‘Dan majalisa.

An yi wa tsofaffi Gwamnoni afuwa

Joshua Dariye wanda ya yi mulki a Filato tsakanin 1999 zuwa 2007, ya fito daga kurkuku bayan ‘yancin da gwamnatin Muhammadu Buhari ta ba shi.

Kara karanta wannan

Ta karewa PDP a Sokoto yayin da fitaccen kwamishina ya kaura, ya koma APC

Sanata Dariye da tsohon gwamnan Taraba, Jolly Nyame sun baro gidan gyaran hali da ke Kuje watanni uku bayan shugaban Najeriya ya yi masu afuwa.

LP za ta kai labari a Filato?

The Guardian tace an kammala komai domin kaddamar da Dariye da zarar ya iso Filato. LP ta ba Alexander Kwapnoe tikitin Sanatan Kudancin Filato.

Ana ganin takarar Dariye a jam’iyyar hamayyar za ta taimakawa Mista Patrick Dakum wanda ya samu tikitin gwamna a LP bayan ya bar jam'iyyar APC.

Shari'ar Ahmed Idris v EFCC

Kun ji labari cewa Lauyan da EFCC ta tura kotu, ya shaidawa Alkali cewa mutanen Ahmed Idris suna neman yin zama da shi domin a sasanta a saukake.

Dama can an saba yin sulhu a wajen kotu ta yadda za a janye kara, shi kuma wanda ake tuhuma zai yi wa hukuma abin da take so a cikin ruwan sanyi.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: APC ta sanar da ranar da za ta fara gangamin yakin neman zaben Tinubu

Asali: Legit.ng

Online view pixel