Gwamnan Benue zai saya wa Yan bijilante bindigogi samfurin AK-47

Gwamnan Benue zai saya wa Yan bijilante bindigogi samfurin AK-47

  • Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom, yace zai sayawa jami’an sabuwar hukumar yan sa kai da ya kaddamar bindodgi kirar AK-47A
  • Samuel Ortom Ya ce yan ta'ada suna kai wa jihar sa hari ne saboda mutanen sa sun ki bayar da filayen su
  • Samuel Ortom ya ce matasa 500 aka zaba daga kananan hokumomi 23 domin shiga kason farko na jami'an tsaron yan sa kai da ya kaddamar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Benue - Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom, yace zai sayawa jami’an sabuwar hukumar yan sa kai da ya kaddamar a jihar bindodgi kirar AK-47A. Rahoton BBC

Samuel Ortom ya bayyana haka ne a jiya Alhamis yayin da yake kaddamar da kungiyar mai suna Community Volunteer Guards a Makurdi

Gwamnan yace gwamnatin jihar Benue za ta bi hanyoyin da ba saba ka'ida ba wajen sayen Ak-47 ga jami'an tsaro.

Ortom
Gwamnan Benue zai saya wa Yan bijilante bindigogi samfurin AK-47 FOTO Legit.NG
Asali: Twitter

Amma Idan gwamatin tarayya taki bashi damar siyawa jami’an yan sakai da ya kaddamar bidigogi zai nemi izinin mutanen sa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na zuwa ne a lokacin da jihohin kamar Ondo, Ekiti, Osun da Zamfara su ka bayyana cewa suma za su baiwa jami'an tsaron jihohinsu bindigogi saboda lalacewar tsaro a jihohin su da kasar baki daya.

Samuel Ortom ya ce yan ta’ada na kaiwa jihar sa Hari ne saboda mutanen sa sun ki bayar da filayen su ga yanta'addan.

Gwamnan ya kara da cewa matasa 500 aka zaba daga kananan hokumomi 23 domin shiga kason farko na jami'an tsaron.

Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci Google Ta Hana IPOB Shiga Dandalin Ta

A wani labari kuma, Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, a ranar Alhamis ya roki kamfanin Google da ta hana mambobin kungiyar ‘yan asalin Biafra (IPOB) damar amfani da dandalinta. Rahoton Daily Trust

Da yake magana jiya a Abuja a lokacin da wata tawagar Google ta ziyarce shi, ya ce:

“haramtattun kungiyar ta’addanci suna amfani da dandalin wajen ayyukan tada kayar baya da kuma tada zaune tsaye.

Asali: Legit.ng

Online view pixel