Yajin aiki: Jami'ar Kaduna ta yi watsi da rikicin ASUU, ta ci gaba da karatu

Yajin aiki: Jami'ar Kaduna ta yi watsi da rikicin ASUU, ta ci gaba da karatu

  • Jami'ar jihar Kaduna ta umarci dukkan malamai da lakcarori su koma karatu duk da yajin aikin ASUU da ake yi
  • Wannan na zuwa ne watanni biyar bayan da kungiyar malaman jami'o'i suka fara yajin aiki saboda wasu dalilai
  • Jami'ar ta Kaduna dai ta bayyana maunufar komawa karatu, kana ta ce tana sa ran malamai da dalibai kowa zai dawo

Jihar Kaduna - Hukumar gudanarwar jami’ar jihar Kaduna (KASU) ta koma karatun zango na biyu na shekarar 2020/2021 ga dalibanta na digirin farko har zuwa digirin digirgir.

Wannan na zuwa ne watanni biyar bayan da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta fara yajin aiki a fadin jami'o'in jiha da ta tarayya a Najeriya, Channels Tv ta ruwaito.

Jami'ar Kaduna ta koma karatu, ta yi watsi da rikici ASUU
Yajin aiki: Jami'ar Kaduna ta yi watsi da rikicin ASUU, ta ci gaba da karatu | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

An koma makarantar ne domin ci gaba da jarrabawar kammala zango na biyu da aka dakatar saboda yajin aikin ASUU da ya fara a watan Fabrairun bana.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Ana ta batun hana acaba, FRSC za ta fara kame wasu nau'ikan babura a Najeriya

Da yake zantawa da gidan Talabijin na Channels, mukaddashin shugaban jami’ar jihar Kaduna Farfesa Abdullahi Ashafa ya bayyana cewa makarantar ba ta da wata rigimar da kungiyar ASUU ta jihar, don haka babu bukatar a ci gaba da ajiye daliban a gida.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya yi gargadin dalibai da malaman da suka ki komawa karatu kamar yadda hukumar jami’ar ta umarta za su fuskanci mummunan sakamako.

A rahoton Legit.ng Hausa na baya, kungiyar malaman jami'o'i (ASUU) ta kara wa'adin yajin aikinta da wata guda domin ba gwamnatin Buhari karin lokacin sake tunanin kawo karshen yajin.

Gwamna El-Rufai ya rantse zai sallami duk Malaman Jami’a da ke yajin-aikin ASUU

A wani labarin, gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yi barazanar korar malaman jami’ar KASU da suka shiga yajin-aikin da kungiyar ASUU ta ke yi.

Kara karanta wannan

Bayan Barazanar Gwamna El-Rufai, Malaman Jami’a Sun Koma Aiki a Kaduna

Jaridar Daily Trust ta rahoto Malam Nasir El-Rufai yana cewa zai kori malaman jami’an jihar Kaduna da suka yi watsi da aikinsu, suka tafi yajin-aiki.

Tun watan Fubrairun shekarar nan kungiyar ASUU ta malaman jami’a take yajin-aiki a kasa, Malaman na zargin gwamnati da kin cika alkawuranta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel