Rundunar 'Yan sandan Najeriya Ta Sanar Da Shirin Daukar Sabbin Dalibai

Rundunar 'Yan sandan Najeriya Ta Sanar Da Shirin Daukar Sabbin Dalibai

  • Rundunar ‘yan sandan Najeriya (NPF) ta gayyaci ‘yan kasa masu sha’awar shiga aikin Dansanda da sun yi rajistar shiga kwalejin Yansanda
  • Za a gudanar da rajistar ne na tsawon makonni shida daga ranar 1 ga watan Agusta zuwa 12 ga watan Satumba
  • Wadanda suka yi nasara za su shiga gwajin na’urar kwamfuta (CBT) da kuma aikin tantance lafiyar jiki

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Rundunar ‘yan sandan Najeriya (NPF) ta gayyaci ‘yan kasa masu sha’awar shiga aikin Dansanda da su yi rajistar shiga kwalejin Karatun dansanda na digiri karo na Tara. Rahoton THE CABLE

Olumuyiwa Adejobi, jami’in hulda da jama’a na rundunar ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.

Olumuyiwa Adejobi ya ce za a gudanar da aikin ragistar ne ta yanar gizo, kuma za a bude wa ‘yan Najeriya masu shekaru 17 zuwa 22.

Kara karanta wannan

2023: Ana Kokarin Kawo Karshen Rikicin Jam’iyyar PDP, Atiku Ya Zauna da Wike

Za a gudanar da rajistar ne na tsawon makonni shida daga ranar 1 ga watan Agusta zuwa 12 ga watan Satumba.

Police
Rundunar 'Yan sanda Najeriya Ta Sanar Da Shirin Daukar Sabin Ma’aikata FOTO Recuritmen board.NG
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin abubuwan da ake bukata sun hada da mallakar lambar shaidar zama dan kasa (NIN) da maki 180 da bai gaza 180 ba a jarabawar JAMB ta shekarar 2022, inda aka zabi makarantar horar da ‘yan sanda ta Najeriya a matsayin cibiyar da aka fi so.

Masu nema dole ne su mallaki mafi karanci makin kiredit 6 a jarabawar WAEC ko NECO da bai wuce zama sau biyu ba, da ku makin kiredit a Math da Ingilishi.

Yan Mata da za su yi rajista Dole su kasance basu da Aure ko juna biyu kuma kada tsayin su yayi kasa da mita 1.64m", su kuma maza kada tsayin su yayi kasa da 86cm (inci 34) na faɗaɗa ƙirji".

Kara karanta wannan

Rashin Kudi Ya Jawo Gwamnoni Sun Ce A Kori Ma’aikata, a Tsuke Bakin Aljihu Kyam

Masu sha'awa za su rajista a yanar gizon Kwalejin kamar haka: https://www.polac.edu.ng, sannan su biya Naira dubu biyar kacal (N5,000) na remitta.

Wadanda suka yi nasara za su shiga gwajin na’urar kwamfuta (CBT) da kuma aikin tantance lafiyar jiki kafin su kai ga mataki na karshe.

Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci Google Ta Hana IPOB Shiga Dandalin Ta

A wani labari kuma, Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, a ranar Alhamis ya roki kamfanin Google da ta hana mambobin kungiyar ‘yan asalin Biafra (IPOB) damar amfani da dandalinta. Rahoton Daily Trust

Da yake magana jiya a Abuja a lokacin da wata tawagar Google ta ziyarce shi, ya ce: “haramtattun kungiyar ta’addanci” suna amfani da dandalin wajen ayyukan tada kayar baya

Asali: Legit.ng

Online view pixel