PDP Ta Zargi Zulum da Gina Manyan Makarantu Da Babu Kwararrun Malamai

PDP Ta Zargi Zulum da Gina Manyan Makarantu Da Babu Kwararrun Malamai

  • Dan takararr gwamna a jam'iyyar PDP ta jihar Borno ya soki Zulum da Gina Manyan Makarantu ba Malamai a fadin Jihar
  • Alhaji Mohammed Jajari ya ce ayyukan gwamna Zulum da ake nunawa Duniya ba haka suke ba a zahiri
  • Jajaeri ya ce ana amfani da yan kwadago wajen gina hanyoyin da basa dadewa kafin su lalace dan azurta abokai da yan uwan Zulum

Jihar Borno - Dan takarar gwamna a jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Borno, Alhaji Mohammed Jajari, ya soki gwamnatin jihar Borno a karkashin Gwamna Babagana Umara Zulum na gina manyan makarantu a fadin jihar ba tare da kwararrun malamai da za su jagoranci makarantun ba. Rahoton LEADERSHIP

Dan takarar gwamnan a jam’iyyar PDP ya ce duk da rashin isassun malamai a jihar, gwamnati ta fara shirin sallamar wadanda ake da su.

Kara karanta wannan

Rikicin siyasa: Tsigaggen mataimakin gwamnan PDP ya ja zuga, masoyansa sun koma APC

Jajari, ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar a ranar Alhamis a Maiduguri.

Zullum
PDP Ta Zargi Zulum da Gina Manyan Makarantu Da Babu Kwararrun Malamai FOTO LEADERSHIP
Asali: Twitter

Dan takarar ya kara da cewa, aikin mayar da yan gudun hijira gidajen su da gwamnatin Zulum ke nunawa duniya yana yi ba haka bane a zahiri.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jajaeri yana mai zargin cewa mafi yawan ‘yan gudun hijirar da suka rasa gidajen su da aka kwashe daga Maiduguri, har yanzu suna sansanoni a hedikwatar kananan hukumomi daban-daban maimakon gidajen su.

Ya kuma zargi gwamnatin jihar da yin amfani da ’yan kwadago kai tsaye wajen gina hanyoyin da suka lalace cikin watanni don kawai a azurtar ‘yan uwa da abokan Zulum.

Yanke Wa Mutane Lantarki Ba Tare Da Ba Su Gargadin Kwana 10 Ba Ya Saba Wa Doka – FCCPC

A wani labari kuma - Yanke wutar Lantarkin mutanen da ba su biya kudi ba ba tare da ba su gargadin kwana goma daga kamfanonin rarraba wuta na DISCO ya sabawa doka inji hukumar Hukumar Kula da Gasa da Kare Hakkin Masu Sayen Kaya ta Kasa (FCCPC).Rahoton Aminiya. DailyTrust

Babatunde Irukera, Mataimakin Shugaban Hukumar FCCPC, ya bayyana haka ne a wani shirin warware korafin masu amfani da wutar lantarki da hukumar FCCPC ta shirya a jihar Kuros Ribas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel