Bidiyo: Gwamna ya dura hedkwatar PDP don a tantance shi ya tsaya takara da Atiku

Bidiyo: Gwamna ya dura hedkwatar PDP don a tantance shi ya tsaya takara da Atiku

  • Jim kadan bayan da aka bayyana cewa, akwai yiwuwar Atiku ya zabi Okowa a matsayin abokin gami, ya dura hedkwatar PDP domin a tantance shi
  • Wannan na zuwa ne daidai lokacin da jam'iyyun siyasa ke ci gaba da bayyana 'yan takararsu na zaben 2023 mai zuwa
  • Jam'iyyar PDP, ta tsayar da Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasa, Okowa kuwa mataimaki

Gwamnan PDP, kuma mai ci a jihar Delta, Ifeanyi Okowa ya dura hedikwatar jam’iyyar PDP da ke Abuja, Channels Tv ta ruwaito.

Zai halarci taron tantance dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar, wanda zai tafi tare da Atiku Abubakar a zabe 2023.

Wasu ‘yan jam’iyyar ne suka tarbe shi cikin ginin hedkwatar da kalaman ‘muna maka murna.'

Kara karanta wannan

Dalilin da Yasa na Darzo Okowa A Matsayin Abokin Takarata a 2023, Atiku Abubakar

Okowa da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike na daga cikin sunayen da aka ambata a matsayin wadanda za su tsaya takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP tare da Atiku Abubakar.

Kalli bidiyon isowarsa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Atiku Abubakar ya Zabi Gwamna Okowa a Matsayin Abokin Tafiyarsa

Atiku Abubakar, 'dan takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP, ya zabi Ifeanyi Okowa, gwamnan jihar Delta a matsayin abokin tafiyarsa a zaben 2023 mai gabatowa, inji Arise Tv.

Kwamitin gudanar da ayyuka na jam'iyyar PDP a ranar Laraba ya zabi Nyesom Wike, gwamnan jihar Ribas, a matsayin wanda zai kasance mataimakin 'dan takarar shugabancin kasan.

Mambobin NWC sun yi zabe inda Wike ya samu kuri'u 13 yayin da Okowa ya samu uku kacal, lamarin da yasa masu ruwa da tsakin suka aminta da Wike.

Kara karanta wannan

Muna bukatar PDP ta koma mulki a 2023: Abokin tafiyar Atiku ya lashi takobi

Sai dai, Atiku Abubkar na gano ya kasa sakin jiki da Wike a matsayin abokin tafiyarsa sabodaya sakankance cewa gwamnan baya kaunarsa.

Okowa: Muhimman abubuwa 12 da baku sani ba game da abokin takarar Atiku a PDP

A wani labarin, mun kawo cewa, a yau ne dan takarar shugaban kasa a PDP, kuma tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar ya bayyana wanda zai tsaya a matsayin mataimakinsa a zaben 2023 mai zuwa.

Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta ne Atiku ya darje ya zaba, daidai lokacin da wa'adin da INEC ta dibarwa jam'iyyu na bayyana 'yan takararsu ke gab da karewa. Waye Okowa? Wannan ita ce tambayar da mutane ka iya neman sanin amsarta.

Legit.ng Hausa ta yi duba ga rayuwarsa da kuma gwagwarmayar siyasarsa domin sanin waye shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel