APC ta shiga Tasku a Kebbi, Sanatocin Jam'iyyar 2, da Wasu Mutum 6 Sun Koma PDP

APC ta shiga Tasku a Kebbi, Sanatocin Jam'iyyar 2, da Wasu Mutum 6 Sun Koma PDP

  • Jam'iyyar APC a jihar Kebbi na fuskantar girgiza inda sanatoci biyu, 'yan majalisar wakilai na tarayya 3 da wasu 'yan majalisar jiha suka sauya sheka
  • Wannan girgizar ta biyo bayan zaben fidda gwanin da aka yi na jam'iyyar APC a jihar wanda mambobinta suka caccaka tare da nuna rashin amintarsu
  • Dukkan manyan 'yan siyasar 8 da suka bar APC sun koma babbar jam'iyyar adawa ya PDP kamar yadda sakataren jam'iyyar a jihar ya tabbatar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kebbi - Jam'iyyar APC a jihar Kebbi ta fara shiga wani hali yayin da ta rasa 'yan majalisar tarayya biyar da 'yan majalisar jiha uku inda suka koma babbar jam'iyyar adawa ta PDP.

Sauya shekar da 'yan jam'iyyar suka yi zuwa PDP ya fara ne byan kammala zaben fidda gwamnin jam'iyyar bayan wadanda suka sauya shekar sun caccaki yanayin zaben fidda gwani da aka yi a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An yi zalunci: Tawagar Yahaya Bello ta caccaki shugabannin APC bisa zaban Tinubu

APC ta shiga Tasku a Kebbi, Sanatocin Jam'iyyar 2, da Wasu Mutum 6 Sun Koma PDP
APC ta shiga Tasku a Kebbi, Sanatocin Jam'iyyar 2, da Wasu Mutum 6 Sun Koma PDP. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Sanata Adamu Aliero mai wakiltar mazabar Kebbi ta tsakiya, shugaban majalisar dattawa, Dr. Yahaya Abdullahi mai wakiltar mazabar Kebbi ta arewa tare da mamban majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kalogo/Bunza a tarayya su ne na farko da suka sanar da sauya shekarsu zuwa PDP.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mohammed Umar Jega da Abdullahi Zumbo, 'yan majalisa masu wakiltar mazabar Aliero/Jega/Gwandu da mazabar Dandi/Arewa a tarayya sun bi sahu inda suka bar APC zuwa PDP.

A wani lamari makamancin hakan, 'yan majalisar jihar, Habibu Labbo mai wakiltar Gwandu, Ismaila Bui mai wakiltar Arewa da Mohammed Buhari Aliero mai wakiltar Aliero, sun bar APC zuwa PDP.

Sakataren PDP na jihar, Usaini Raha, ya tabbatar da wannan sauya shekar ta 'yan majalisun.

A kan rade-radin sauya shekar tsohon gwamnan jihar, Sa'idu Usman Dakingari, zuwa PDP, Raha ya ce har yanzu bai samu bayanin hakan ba.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Malik Ado-Ibrahim ya lashe tikitin takarar a YPP ta su Adamu Garba

Nwajiuba ya bayyana dalilinsa na rashin zuwa Eagle Sqaure duk da yana takara

A wani labari na daban, Chinedu Nwajiuba, kanin karamin ministan ilimi kuma 'dan takarar shugabancin kasa a karkashin jam'iyyar APC, Emeka Nwajiuba, ya yi bayanin dalilin da ya hana yayansa halartar zaben fidda gwani da ake yi a Eagle Square, Abuja.

Kanin Nwajiuba ya ce yayan shi ya ki zuwa filin taron ne saboda shugabancin jam'iyyar APC ya ci amanarsa.

Ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar daren jiya, 7 ga watan Yuni kuma Legit.ng ta gani.

An kira sunan Nwajiuba babu adadi domin ya fito yayi jawabi ga jama'ar da suka halarci gangamin taron fidda gwanin amma shiru ka ke ji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel