Zaben Fidda Gwani: Akwai Babban Hatsari da ke Kunno kai, NWC ga Tinubu da Sauran 'yan takarar Kudu

Zaben Fidda Gwani: Akwai Babban Hatsari da ke Kunno kai, NWC ga Tinubu da Sauran 'yan takarar Kudu

  • Shugaban matasan jam'iyyar APC na kasa, Dayo Israel ya ja kunnen 'yan takarar shugaban kasar jam'iyyar da shugabannin siyasa daga kudu a kan rashin hadin kai inda yace babbar matsala na nan tafe
  • Yace 'yan takarar shugaban kasar jam'iyyar na tsaka mai wuya yayin da jam'iyyar ke zaben fidda gwaninta a yau bayan gwamnonin jam'iyyar APC na arewa sun bukaci a mika mulki ga kudu
  • Hakan yazo ne bayan mambobin kwamitin ayyuka na kasa sun yi watsi da Ahmad Lawan a matsayin wanda shugaban jam'iyyar ya nada bayan tuntubar Buhari game da wanda zai gaje shi

FCT, Abuja - Shugaban matasan jami'iyyar APC na kasa, Dayo Israel ya ja kunnen 'yan takarar shugaban kasa da shugabannin siyasar kudu a kan rashin hadin kai.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Rikici a APC yayin da ake yunkurin magudi a jerin sunayen deliget

Kamar yadda ya ce, akwai 'yan takarar shugaban kasa na kudu suna tsaka mai wuya a zaben fidda gwanin jam'iyyar da ake yi.

Zaben Fidda Gwani: Akwai Babban Hatsari da ke Kunno kai, NWC ga Tinubu da Sauran 'yan takarar Kudu
Zaben Fidda Gwani: Akwai Babban Hatsari da ke Kunno kai, NWC ga Tinubu da Sauran 'yan takarar Kudu. Hoto daga @OfficialAPCNg
Asali: UGC

Israel ya bukaci 'yan takarar su girmama darajar gwamnonin arewa wajen mika mulki ga kudu.

Daga cikin 'yan takarar kudu sun hada da jagoran APC na kasa, Bola Tinubu, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, "Ya kamata 'yan takarar shugaban kasa na kudu su hada kawunansu duba da yadda gwamnonin arewa suka bukaci mika mulki shugabancin kasa ga yankin kudu.
"Ya isa kowa ishara. Ewu mbe loko longe (akwai matsala)."

The Punch ta ruwaito yadda gwamnonin APC na arewancin Najeriya suka goyi bayan mika mulki ga kudu.

Haka zalika, gwamnonin jam'iyyar APC na arewa sun bukaci 'yan takarar shugaban kasa daga arewa su janye.

Kara karanta wannan

Ana Dab da Fara Zaben Fidda Gwani, Buhari ya Aika Muhimmin Sako ga Deliget

"Saboda haka ne muke matukar bukatar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemi wanda zai gaje shi a matsayin 'dan takarar shugaban kasar APC daga 'yan uwanmu na jihohin kudu.
"Muna rokon dukkan 'yan takarar daga jihohin arewa da su janye ra'ayinsu na shugabancin kasa gami da barin 'yan takarar kudu kadai a matsayin wadanda jam'iyyar za ta bawa tikiti," a cewar gwamnonin.

Har ila yau, Israel ya kara da bayyana yadda mambobin kwamitin ayyuka na kasa suka ki amincewa da Ahmad Lawan a matsayin 'dan takarar da jam'iyyar ta tsayar.

Yayin da shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Adamu ya yi yunkurin daukar shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan - 'dan arewa - a matsayin 'dan takarar da za a ba wa tiketin tsayawa takarar shugaban kasa a APC, bai yi tasiri ba a ranar Litinin saboda yadda fadar shugaban kasa da gwamnonin arewa 12 na jam'iyyar suka fito karara suka nuna rashin amincewarsu.

Kara karanta wannan

Taron APC: Har yanzu Buhari bai zartar da hukunci kan mika mulki kudu ba - Badaru

Bayan ganawar, Adamu ya yi hanzari fadawa motarsa tare da yin layar zana.

Bayan wani 'dan lokaci da gabatar da taron NWC, kimanin bakwai daga cikin gwamnonin karkashin jagorancin sakataren tsara ayyuka na APC, Suleiman Argungu, ya shaidawa manema labarai a sakateriyar jam'iyyar cewa Lawan bai cancanci a bashi tikitin tsayawa takara a jam'iyyar ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel