Ana Dab da Fara Zaben Fidda Gwani, Buhari ya Aika Muhimmin Sako ga Deliget

Ana Dab da Fara Zaben Fidda Gwani, Buhari ya Aika Muhimmin Sako ga Deliget

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga wakilan zaben fidda gwani da su yi kokarin ganin sun sauke nauyin da ke wuyansu ba tare da an juya ko canza musu ra'ayi ba
  • A cewar Buhari, dole ne su tsaida 'dan takarar da zai rike tutar jam'iyyarsu don ganin an yi nasara a shekara mai zuwa tare da duba cancanta
  • Haka zalika, ya kara da cewa ya kamata sakamakon zaben fidda gwanin ya tabbatar da irin damakaradiyyar da APC ke gudanarwa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce wakilan zaben fidda 'dan takarar shugaban kasar jam'iyyar APC suyi kokarin sauke nauyin da ke wuyansu ba tare da an cusa ko juya musu ra'ayi ba.

Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban kasa ya yanko maganar da Buhari ya fadi a wata takarda da ta fita ranar Litinin, The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023 ce Shekarar da Karyarku Za Ta Kare, Atiku Abubakar ga APC

Ana Dab da Fara Zaben Fidda Gwani, Buhari ya Aika Muhimmin Sako ga Deliget
Ana Dab da Fara Zaben Fidda Gwani, Buhari ya Aika Muhimmin Sako ga Deliget. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Zaben fidda 'dan takarar shugaban kasar wanda za a gabatar a ranar 7 ga watan Yuni ya riga ya kankama.

Yayin da Abdullahi Adamu, shugaban jam'iyyar APC na kasa ya ayyana shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan a matsayin 'dan takarar shugaban kasar jam'iyyar, gwamnonin jam'iyyar sun hakikance a kan cewa dole a ba kudu tikitin tsayawa takarar shugaban kasar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Amma Buhari ya ce sakamakon zaben fidda gwanin jam'iyyar APC ya nuna cewa jam'iyyar damokaradiyya ce.

"Kamar yadda na gana da gwamnonin jam'iyyar a makon da ya gabata, ya kamata sakamakon zaben fidda gwanin jam'iyyar ya nunawa duniya tsarin damakaradiyyar da jam'iyyar APC ke gudanarwa," a cewarsa.
"Dole ne mu nuna hakan a dukkan lamurra da tsarin rayuwarmu. Ginshikan jam'iyyar wadanda su ne madogararmu tun daga lokacin da aka kafa jam'iyyar, zuwa zaben farko da aka yi nasara, na biyu a 2019 da na uku cikin taimakon Allah a shekarar 2023." A cewarsa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Buhari ya magantu kan hanyar da za a bi wajen zabar dan takarar APC

Ya ce, wakilan zaben su yi kokarin ganin sun zabi wanda ya dace gami da daukar wanda zai rike tutar jam'iyyar don ganin an yi nasara a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel