Magajin Buhari: Zamu shiga tasku idan muka gaza zakulo ɗan takara mai ƙarfin Atiku, Gwamnan APC

Magajin Buhari: Zamu shiga tasku idan muka gaza zakulo ɗan takara mai ƙarfin Atiku, Gwamnan APC

  • Gwamnan Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce APC zata shiga matsala idan ba ta tsayar da wanda zai iya ja da Atiku ba
  • Gwamnan ya ce ɗan takarar da PDP ta tsayar sananne ne kuma mai karfi dan haka wajibi APC ta yi karatun tanatsu
  • Zuwa yanzun an fara aiwatar muhimman abubuwa a filin taron APC tun bayan isar shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari

Abuja - Gwamnan Abdullahi Sule na jihar Nasarawa, ya ce ayyana Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar PDP shi ne zai ƙayyade matakin da APC zata ɗauka nan da yan awanni.

Gwamna Sule ya yi wannan furucin ne yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a wurin taron APC ranar Talata, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sanatan APC: Yan takara uku sun janye wa mataimakin shugaban ƙasa Osinbajo

Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule.
Magajin Buhari: Zamu shiga tasku idan muka gaza zakulo ɗan takara mai ƙarfin Atiku, Gwamnan APC Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

An kammala duk wasu shirye-shirye na fara kaɗa kuri'a domin zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC a Filin Eagle Square.

Gwamnan ya bayyana cewa babbar jam'iyyar hamayya ta ƙasa PDP ta tsayar da ɗan takara mai ƙarfi kuma sananne ga kowane mutum a faɗin duniya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake jawabi ga manema labarai, Gwamna Sule ya ce:

"Wajibi mu fitar da ɗan takarar da zai gogayya da Atiku kuma ya lallasa shi, duk wani mataki da ba wannan ba, mu a jam'iyyance mun shiga gagarumar matsala."
"Saboda haka duk wani mataki na zaɓen ɗan takara zai dogara ne da wanda muke hange."

Abubuwan sun kankama bayan isar Buhari Eagle Square

Tun bayan isar shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, filin taron APC, tuni dai aka fara gudanar da ayyukan da aka tsara don zaɓo ɗan takara.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Babbar Kotu ta soke zaɓen fidda ɗan takarar gwamna na jam'iyyar PDP

Shugaban jam'iyya na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya yi jawabin buɗe taro, inda ya tabbatar da cewa APC ta faɗa cikin rikici ba.

A wani labatrin na daban kuma Shugaba Buhari ya magantu kan kowane ɗaya daga cikin yan takara 5 da gwamnoni suka kai masa

Gwamnan Filato, Simon Lalong, ya ce shugaban ƙasa Buhari ya aminta da dukkan yan takara 5 da muka kai masa gabanin fara zaɓe.

Gwamnan wanda ke jagorantar gwamnonin arewa ya ce ba zai yuwu su tafi wurin zabe da dukkanin yan takara ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel