2023: Atiku Abubakar ya dira Hedkwatar jam'iyyar PDP ta ƙasa zai karbi tikitin takarar shugaban ƙasa

2023: Atiku Abubakar ya dira Hedkwatar jam'iyyar PDP ta ƙasa zai karbi tikitin takarar shugaban ƙasa

  • Kwamitin gudanar NWC na jam'iyar PDP ta ƙasa ya baiwa Atiku Abubakar tikitin takarar shugaban kasa a zaɓen 2023 da ke tafe
  • Shugaban PDP, Mista Ayu, ya bayyana Atiku da mutumin da ya ga jiya kuma ya ga yau kuma shugaban kasan gobe
  • Da yake jawabi a wurin, Atiku Abubakar, ya nemi mambobin PDP su haɗa kai domin caimma nasara a zaɓen da ke tafe

Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa karkashin PDP a zaben 2023 dake tafe, Atiku Abubakar, ya dira Hedkwatar jam'iyya ta ƙasa da ke Abuja ranar Laraba domin karban tikitin takara.

Channels TV ta ruwaito cewa Atiku zai karɓi takardan shaidar cin zaɓe da zama ɗan takara daga wurin kwamitin gudanarwa NWC na PDP ta ƙasa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: APGA ta sanar da sakamakon zaɓen fidda gwanin ɗan takarar shugaban ƙasa

Atiku Abubakar.
2023: Atiku Abubakar ya dira Hedkwatar jam'iyyar PDP ta ƙasa zai karbi tikitin takarar shugaban ƙasa Hoto: BBC Pidgin/facebook
Asali: Facebook

Sauran jiga-jigan da aka hanga a Hedkwatar jam'iyyar sun haɗa da yan takarar da suka fafata da tsohon mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen fidda gwanin da aka kammala.

Daga cikin waɗan sa suka halarci wurin har da, Sanata Bukola Saraki, Sam Ohuabunwa, Nwachukwu Anakwenze da kuma Mohammed Hayatu-Deen.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Babban abokin hamayyar Atiku yayin zaɓen fitar da gwani wato gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas bai halarci wurin ba zuwa lokacin da muke haɗa rahoton.

PDP ta bai wa Atiku tikitin takitin takarar shugaban kasa

Jam'iyyar PDP ta damƙa wa Atiku Abubakar shaidar zama ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaben 2023 bayan lashe zaɓen fid da gwani, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Atiku, wanda ya karbi shaidar ranar Laraba a Abuja, ya samu kuri'u 371, wanda ya ba shi damar lashe tikitin da zai kare martabar PDP a zaɓen.

Kara karanta wannan

Ana shirin tunkarar zaɓe, Jiga-Jigai da mambobin jam'iyyar hamayya 1,000 sun sauya sheƙa zuwa APC

Gwamna Wike na jihar Ribas ne ya zo na biyu da kuri'u 237, yayin da Bukola Saraki ya zo na uku da Kuri'u 70, sai kuma gwamna Udom Emmanuel da 38.

Da yake jawabi a wurin, shugaban PDP na ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu, ya bayyana Atiku da, "Mutumin da ya ga jiya kuma yake ganin yau," kuma ya kara da cewa shi ne shugaban ƙasan Gobe.

A nashi jawabin Atiku, ya yaba wa jam'iyya bisa rashin nuna wariya yayin zaɓen fidda gwani na takarar shugaban ƙasa.

Tsohon mataimakin shugaban kasan ya kuma bukaci mambobin PDP a lungu da sako su yi aiki tare domin cimma nasara a zaɓen 2023.

A wani labarin kuma APGA ta sanar da sakamakon zaɓen fidda gwanin ɗan takarar shugaban ƙasa

Jam'iyyar APGA ta tsayar da Farfesa Peter Umeadi a matsayin ɗan takarar kujerar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.

A wurin taron zaɓen fidda gwani da ta shirya a hedkwatar jam'iyyar ta kasa, akalla Deleget 150 ne suka tabbatar da takarar Umeadi.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya faɗa mana ɗan takarar da yake son ya gaje shi a 2023, Gwamnan arewa ya fasa kwai

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262