Mambobin jam'iyyar hamayya sama da 1,000 sun sauya sheƙa zuwa APC a Ekiti

Mambobin jam'iyyar hamayya sama da 1,000 sun sauya sheƙa zuwa APC a Ekiti

  • Yayin da jam'iyyu ke shirin tunkarar babban zaɓen gwamna a watan Yuni 2022, APC mai mulki ta samu gagarumin goyon baya a Ekiti
  • Shugaban jam'iyyar LP da mambobi 1,000 sun sauya sheƙa zuwa APC, sun yaga katin su sun karɓi tsintsiya
  • Sun sha alwashin aiki ba dare ba rana wajen samun nasarar ɗan takarar sabuwar jam'iyyarsu a zaɓen gwamnan da ke tafe

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ekiti - Jam'iyyar APC reshen jihar Ekiti, ranar Talata, ta samu gagarumin ƙarin karɓuwa yayin da mambobin jam'iyyar Labour Party 1,000 suka sauya sheka zuwa jam'iyya mai mulki.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa masu sauya shekar sun fito ne daga dukkanin kananan hukumomi 16 da suka haɗa jihar Ekiti.

Ɗaruruwan masu sauya sheƙan sun sha alwashin aiki ba dare ba rana domin nasarar ɗan takarar gwamna karƙashin APC, Biodun Abayomi Oyebanji.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: APGA ta sanar da sakamakon zaɓen fidda gwanin ɗan takarar shugaban ƙasa

Tutar jam'iyyar APC.
Mambobin jam'iyyar hamayya sama da 1,000 sun sauya sheƙa zuwa APC a Ekiti Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Shugaban ƙungiyar kamfen ɗin ɗan takarar gwamnan Ekiti, Chief Olajide Awe, ne ya tarbi sabbin mambobin APC a wani taro da aka shirya na musamman a Ado Ekiti.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Karƙashin jagorancin shugaban jam'iyyar LP na jiha, injiniya Banji Omotoso, mutanen sun ce kwarewa da kyakkyawar mu'amalar Oyebanji ce ta jawo hankalinsu suka yanke shawarar komawa APC.

A cewarsu, ɗan takarar yana da cikakkiyar kwarewar da zai ɗora daga cigaban da al'umma suka gani a jihar Ekiti.

A wurin taron an raba wa dukkan masu sauya shekan tsintsiya wato alama ta sabuwar jam'iyyarsu, yayin da su kuma suka yaga Katin jam'iyyar LP don tabbatar da ficewarsu.

Kun zama ɗaya da kowane mamba a APC - Awe

Da yake jawabi a wurin taron, Mista Awe, wanda ya yi maraba da sauya shekar su a dai-dai lokaci mai muhimmanci, ya tabbatar musu cewa ba za'a nuna musu banbanci ba.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari ya ce zai zaɓi wanda zai gaje shi a 2023, ya nemi goyon bayan gwamnoni

Mista Awe ya ce:

"Muna mai ƙara jaddada cewa da zaran ka koma APC, ka zama cikakken mamba duk wata dama da alfarma kana da ita dai-dai da tsofaffin mambobi. Kana da damar shiga harkokin jam'iyya."

A wani labarin kuma Jam'iyyar NNPP ta baiwa Rabiu Kwankwaso tikitin takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023

Jam'iyya mai tashe wato NNPP mai kayan marmari ta damƙa wa Sanata Kwankwaso tikitin takarar shugaban ƙasa a 2023.

Kwankwaso karkashin sabuwar jam'iyyar zai fafata da sauran yan takara musamman na manyan jam'iyyu PDP da APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel