Da Dumi-Dumi: Jam'iyyar APGA ta sanar da sakamakon zaɓen fidda gwanin ɗan takarar shugaban ƙasa

Da Dumi-Dumi: Jam'iyyar APGA ta sanar da sakamakon zaɓen fidda gwanin ɗan takarar shugaban ƙasa

  • Jam'iyyar APGA ta tsayar da Farfesa Peter Umeadi a matsayin ɗan takarar kujerar shugaban ƙasa a zaɓen 2023
  • A wurin taron zaɓen fidda gwani da ta shirya a hedkwatar jam'iyyar ta kasa, akalla Deleget 150 ne suka tabbatar da takarar Umeadi
  • Da yake jawabin godiya, Farfesa Umeadi ya ce idan ya zama shugaban ƙasa zai ɗaga Najeriya kowa ya yi alfahari da ita

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Farfesa Peter Umeadi, ya lashe tikitin takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar All Progressive Grand Alliance, APGA a wurin taron zaben fidda gwani.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa taron na musamman ya samu halartar shugabanni da mambobin APGA daga shiyyoyin Najeriya shida.

A wurin taron, wanda ya gudana a hedkwatar APGA ta ƙasa da ke Katampe-Abuja, adadin Deleget 150 ne suka tabbatar da takarar Farfesa Umeadi ta hanyar kaɗa kuri'ar murya.

Kara karanta wannan

2023: Jam'iyyar SDP Ta Tsayar Da Gogaggen Sanata Takarar Shugaban Kasa

Farfesa Peter Umeadi.
Da Dumi-Dumi: Jam'iyyar APGA ta sanar da sakamakon zaɓen fidda gwanin ɗan takarar shugaban ƙasa Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A jawabinsa, shugaban jam'iyyar APGA na ƙasa, Chief Victor Oye, ya gode wa mambobin jam'iyyar bisa share dogon zango na tafiya daga sassan ƙasar nan don su halarci taron.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya kuma bayyana yaƙinin cewa a shekarar 2023 da ke tafe za'a rantsar da Farfesa Umeadi a matsayin sabon shugaban ƙasa na tarayyan Najeriya.

A ɓangarensa, Farfesa Umeadi ya ɗauki alkawarin ɗaga martabar Najeriya zuwa babban matsayi ta yadda kowane ɗan Najeriya zai bugi ƙirji yana alfahari da ƙasarsa, idan aka zaɓe shi ya zama shugaban ƙasa.

Jam'iyyar PDP da SDP sun tsayar da ɗan takara

Idan baku manta ba a ranar Asabar da ta gabata, tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya lashe zaɓen fidda gwani na ɗan takarar shugaban ƙasa a PDP.

Atiku ya lallasa sauran yan takarar da suka fafata biyo bayan wata kara da Gwamna Tambuwal ya masa, inda ya janye kuma ya umarci masoyansa su zaɓi Atiku

Kara karanta wannan

Ana shirin tunkarar zaɓe, Jiga-Jigai da mambobin jam'iyyar hamayya 1,000 sun sauya sheƙa zuwa APC

Haka nan kuma, Sanata Ebenezer Ikeyina, a ranar Talata ya zama dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Social Democratic Party (SDP).

Shugaban Kwamitin Shirya Taron Jam'iyyar, Mike Odunrinde, wanda ya jagoranci zaben fidda gwani na jam'iyyar a Abuja, ya ce cikin daliget 311 da aka tantance, 308 sun zabi Ikeyina wanda ya wakilci Anambra ta Tsakiya a Majalisa.

A wani labarin kuma Shugaba Buhari ya ce zai zaɓi wanda zai gaje shi a 2023, ya nemi goyon bayan gwamnoni

Shugaba Buhari ya nemi goyon bayan gwamnonin APC yayin da yake shirin zaɓar ɗan takarar da yake fatan ya gaje shi a 2023.

Yayin ganawarsa da gwamnonin kafin tafiyarsa Sufaniya, Buhari ya ce zai duba wasu muhimman abu kafin ya goyi bayan ɗan takara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel