Da Dumi-Dumi: Mako ɗaya bayan Murabus, Ministan Buhari ya lashe tikitin gwamna a APC

Da Dumi-Dumi: Mako ɗaya bayan Murabus, Ministan Buhari ya lashe tikitin gwamna a APC

  • Tsohon ministan haƙar ma'adanai da ƙarafa, Uche Ogah, bai rasa baki ɗaya ba bayan ya yi murabus daga kujerarsa
  • A ranar 27 ga watan Mayu, 2022 aka bayyana Ogah a matsayin wanda ya lashe tikitin takarar gwamnan jihar Abia na APC
  • Daga cikin kuri'u 195,801 da aka kaɗa a zaɓen, Ogah ya samu kuri'u 141,952 kuma shi baturen zaɓe ya sanar ya lashe zaɓe

Abia - Tsohon ministan haƙar ma'adai da cigaban ƙarafa da ya sauka, Uche Ogah, ya lashe tikitin takarar gwamnan jihar Abia na jam'iyyar APC.

Ogah, bayan gudanar da zaben fitar da gwani ta hanyar ƙato bayan ƙato ranar Jumu'a 27 ga watan Mayu, 2022, ya samu kuri'u 141,952 daga cikin kuri'u 195,801da aka kaɗa, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Ɗan Ministan Buhari ya sha kaye a zaben fidda gwanin jam'iyyar APC

Uche Ogah.
Da Dumi-Dumi: Mako ɗaya bayan Murabus, Ministan Buhari ya lashe tikitin gwamna a APC Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

Baturen zaɓen jihar, Perfect Okorie, ya bayyana tsohon Ministan a matsayin wanda ya lashe zaɓen kuma a cewarsa an gudanar da zaɓe mai inganci.

Ogah ya yi godiya bayan samun nasara

Da yake jawabi bayan bayyana sakamako, Ogah ya gode wa mambobin jam'iyyar APC da suka kaɗa kuri'unsu bisa yarda da shi, inda ya ƙara da cewa ba zai ba su kunya ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ɗan takarar gwamnan Abia karkashin APC ya ce ya sadaukar nasarar da ya samu ga Allah, inda ya ƙara da cewa yana da kwarin guiwar zai samu nasara a zaɓen 2023.

A kwanakin baya, shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya umarci ministocinsa da sauran naɗe-naɗensa waɗan da ke da burin tsayawa takara su yi murabus.

Wasu daga cikin ministoci sun bi umarnin shugaban sun aje aiki amma wasu kuma sai suka janye daga takarar da suka yi nufin yi a 2023.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Dr Dikko Radda ya lashe zaben fidda gwanin APC a jihar shugaban ƙasa

A wani labarin kuma Wani Ɗan majalisar jiha ya sauka sheƙa daga NNPP zuwa jam'iyyar APC a Kano

Wani ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Dawakin Kudu a Kano ya sauya sheka daga jam'iyyar NNPP zuwa APC mai mulki.

Honorabul Muazzam El-Yakuba, ya tabbatar da sauya shekarsa ne a wata takarda da ya aike wa majalisar dokokin jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel