Wani Ɗan majalisar jiha ya sauka sheƙa daga NNPP zuwa jam'iyyar APC a Kano

Wani Ɗan majalisar jiha ya sauka sheƙa daga NNPP zuwa jam'iyyar APC a Kano

  • Wani ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Dawakin Kudu a Kano ya sauya sheka daga jam'iyyar NNPP zuwa APC mai mulki
  • Honorabul Muazzam El-Yakuba, ya tabbatar da sauya shekarsa ne a wata takarda da ya aike wa majalisar dokokin jihar Kano
  • A farkon wannan makon ne ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Kwankwaso wato Madobi ya koma APC tare da wasu uku

Kano - Mamba a majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar mazaɓar Dawakin Kudu, Honorabul Mu’azzam El-Yakuba, ya fice daga jam'iyyar NNPP mai kayan marmari, ya koma APC mai mulki.

Daily Trust ta rahoto cewa a farkon wannan watan ne ɗan majalisar tare da wasu takwarorinsa Tara suka sauya sheƙa daga PDP zuwa jam'iyyar NNPP da ke tashe a Kano.

Siyasar Kano.
Wani Ɗan majalisar jiha ya sauka sheƙa daga NNPP zuwa jam'iyyar APC a Kano Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Amma a ranar Jumu'a 27 ga watan Mayu, ɗan majalisar ya mika takaradar sauya sheka ga majalisar dokokin jihar.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Ɗan Ministan Buhari ya sha kaye a zaben fidda gwanin jam'iyyar APC

Daraktan yaɗa labarai na majalisa, Uba Abdullahi, ya bayyana cewa El-Yakuba ya sanarwa majalisa cewa shi da ɗumbin magoya bayansa sun koma APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Ɗaan majalisar ya bayyana cewa shi da dandazon magoya bayansa sun sauya sheƙa zuwa APC kuma yana fatan majalisa ta san da samun wannan cigaban."
"Bayan haka ya sha alwashin yin aiki tare da sauran mambobin jam'iyya don cigaba da samun nasarar APC a faɗin jihar Kano."

Abdullahi ya ƙara da cewa majalisa ta karɓi takardar ɗan majalisan kuma ta masa fatan Alkairy a harkokin siyasar da ya tasa na gaba.

Legit.ng Hausa ta rahoto muku yadda a farkon makon nan, ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Kwankwaso wato Madobi tare da da wasu takwarorinsa uku suka sauya sheka daga NNPP zuwa APC.

A wani labarin na daban kuma Ɗan Ministan Buhari ya sha kaye a zaben fidda gwanin jam'iyyar APC

Kara karanta wannan

‘Dan tsohon Gwamnan da ya rasu, Surukin Ganduje ya lashe zaben takarar ‘Dan Majalisa

Folajimi Mohammed, ɗan ministan yada labarai da Al'adu, Alhaji Lai Muhammed, ya rasa tikitin wakiltar mazaɓar Ikeja 1 a majalisar dokokin jihar Legas.

Ɗan ministan, wanda yanzu haka ya ke kan kujerar ɗan majalisar jiha a karo na biyu ya gaza samun tikitin ta zarce, inda ya sha kaye da zaɓen fid da gwanin jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel