Jam'iyyar APC ta sanya ranar fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa, gwamnoni da yan majalisu

Jam'iyyar APC ta sanya ranar fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa, gwamnoni da yan majalisu

  • Jam'iyya mai mulki Najeriya ta sanya ranar da zata gudanar da zaɓen fitar da ɗan takararta na shugaban ƙasa a 2023
  • Haka nan APC ta sanya ranar zaɓen fitar da yan takarar gwamna a jihohi 36, da yan majalisun dokoki da na tarayya
  • Zaɓukan za su gudana baki ɗaya a watan Mayu, 2022, duk a wani bangare na shirin tunkarar babban zaɓe

Abuja - Jam'iyyar APC ta zaɓi ranar 30 ga watan Mayu, 2022 a matsayin ranar da zata gudanar da zaben fidda gwani na takarar shugaban ƙasa. Haka nan ta fara shawara kan zabukan fidda yan takara na sauran kujeru.

Jam'iyya mai mulki ta kara da cewa ta fara shirin gudanar da zaɓen fitar da gwani na yan takarar majalisun dokoki na johohin ƙasar nan a ranar 17 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Daga karshe, Gwamna Ortom ya fayyace yankin da PDP zata ba takarar shugaban ƙasa a 2023

Kazalika ta fara shirin zaben fitar da yan takarar kujerun majalisar wakilan tarayya a ranar 19 ga watan Mayu, 2022, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

Tutar jam'iyyar APC mai mulki.
Jam'iyyar APC ta sanya ranar fitar da ɗan takarar shugaban masa, gwamnoni da yan majalisu Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

A cewar APC, zaɓen fitar da yan takarar kujerun majalisar dattawan Najeriya a dukkan faɗin kasar nan zai zo ranar 21 ga watan Mayu, yayin da na gwamnoni ta zaɓi 24 ga watan Mayu.

Wannan cigaban na zuwa ne makonni kaɗan bayan APC ta kammala babban gangamin taro na ƙasa, inda ta zaɓi mambobin kwamitin ayyuka (NWC) yayin da ta fara shirin fuskantar babban zaɓen 2023.

APC ta shirya tsaf

Yayin taron wanda aka gudanar da zaɓen shugabanni ta hanyar sulhu, an bayyana Sanata Abdullahi Adamu a matsayin Ciyaman, aka tabbatar da snaata Iyiola Omisore, a matsayin Sakatare na ƙasa.

Kara karanta wannan

Jerin sharuddan da INEC ta gindaya wa jam'iyyun siyasa, ta shirya fatali da yan takara a zaɓen 2023

Wasu yan kwanaki bayan haka, Sanata Adamu, ya karɓi ragamar jam'iyya a hannun shugaban riko mai barin gado, Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe.

Sabon shugaban APC ya sha alwashin ɗora jam'iyya kan turban nasara kuma ya bukaci yan Najeriya su cigaba da goyon bayan APC a kokarinta na kawo cigaba.

Sabon shugaban ya ce:

"Jam'iyyar APC ta shirya tsaf wajen yin abubuwa da yawa idan yan Najeriya suka cigaba da nuna mana soyayya, goyon baya da ƙwarin guiwarsu a babban zaɓe mai zuwa."

A wani labarin kuma Shugaban matasan jam'iyyar APC a Uk ya yi murabus, ya koma NNPP mai kayan marmari

Shugaban matasan APC reshen yan Najeriya mazauna Burtaniya ya yi murabus daga mukaminsa, ya koma NNPP.

Dakta Usman Shehu, ya ce tsohuwar jam'iyyarsa ta gaza cika wa yan Najeriya alƙawurran da ta ɗauka a yaƙin neman zaɓe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel