Da Dumi-Dumi: Kwamitin karba-karɓa na PDP bai buɗe kofa kowa ya nemi takara ba, gwamna Ortom

Da Dumi-Dumi: Kwamitin karba-karɓa na PDP bai buɗe kofa kowa ya nemi takara ba, gwamna Ortom

  • Shugaban kwamitin karba-karba na jam'iyyar PDP ya musanta rahoton cewa sun buɗe kofa kowa ya nemi takara a zaɓen 2023
  • Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai, ya ce sun kammala aikinsu kuma sun kai wa NEC rahoto, wuƙa da nama na hannunta
  • Ortom ya ce a matsayinsa na shugaban kwamiti, mutane sun yi wa maganarsa gurguwar fahimta

Benue - Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai, ya ce kwamitin tsarin karɓa-karɓa na jam'iyyar PDP bai bar kofa ga kowa ya nemi tikitin rakarar shugaban ƙasa ba.

The Cable ta rahoto cewa Ortom, wanda ke jagorantar Kwamitin, ya yi wannan karin hasken ne a wata sanarwa da sakataren watsa labaransa, Nathaniel Ikyur, ya fitar ranar Laraba.

Gwamnan Benuwai, Samuel Ortom.
Da Dumi-Dumi: Kwamitin karba-karɓa na PDP bai buɗe kofa kowa ya nemi takara ba, gwamna Ortom Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

A cewar sanarwan, gwamna Ortom ya yi karin bayani da fayyace gaskiya kan lamarin ne yayin da ya bayyana a cikin shirin 'Morning Show' na kafar Arise TV.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Shugaba Buhari ya rattafa hannu kan sabuwar dokar wajabta kula da ofishoshin gwamnati

Gwamnan ya ce kwamitinsa ya miƙa rahotonsa da shawarwari ga kwamitin ƙoli na PDP ta ƙasa (NEC) domin ɗaukar mataki na gaba. Inda ya ƙara da cewa ba'a fahimci jawabinsa kan lamarin ba.

Ortom ya ce:

"Ina son yin ƙarin haske kan rahoton cewa kwamitin karɓa karɓa ya bar kofa a buɗe kowane yanki ya nemi tikitin shugaban ƙasa a PDP."
"A jiya na sanar da manema labarai cewa Kwamiti ya cimma matsaya ɗaya da zai gabatarwa majalisar koli (NEC) ta jam'iyya. A ina nace Kwamitin ya buɗe kofa kowa ya nemi tikiti?"
"Kwamiti zai gabatar da rahotonsa ga NEC kuma majalisar ce kaɗai ke da karfin ikon yanke hukunci kan tsarin karba-karba."

Wane yanki kwamitin ya kai takarar shugaban ƙasa?

Ortom ya bayyana cewa kamar yadda kowa ya sani an samu kace-nace kan yanki, wasu na ganin ɗan kudu ya kamata a ba takara wasu kuma na ganin ɗan arewa.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: PDP tayi watsi da tsarin karba-karba, tace kowa zai iya takaran kujeran shugaban kasa

Haka nan a cewar gwamnan, akwai mambobin kwamitin dake ganin a bar neman takarar a buɗe kowa ya gwada sa'arsa, har a zabi wanda ya fi dacewa.

Sai dai a matsayin shugaban kwamitin, gwamna Ortom ya musanta cewa sun yanke buɗe kifa kowa ya nemi takara.

"Mun miƙa rahoto ga NEC, ba dai-dai bane kafafen labarai sun yanke hukunci duk da ba su a cikin mambobin wannan kwamiti."

A wani labarin kuma Hadimin Sule Lamido da wasu jiga-jigan PDP sun fice daga jam'iyya, sun koma NNPP ta Kwankwaso

Jam'iyyar NNPP mai kayan marmari ta samu karin mambobin PDP a jihar Jigawa, waɗan da suka sauya sheƙa zuwa cikinta.

Tsohon hadimin tsohon gwamna Sule Lamiɗo, Lawan Kazaure, shi ya jagoranci masu sauya sheƙar zuwa sabuwar jam'iyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262