‘Dan cikin tsohon Gwamna kuma Sanata mai-ci a PDP zai yi takarar ‘Dan Majalisa a 2023

‘Dan cikin tsohon Gwamna kuma Sanata mai-ci a PDP zai yi takarar ‘Dan Majalisa a 2023

  • Pam Jonah Jang zai yi takarar ‘Dan majalisa mai wakiltar yankin Jos a majalisar wakilan tarayya
  • Wasu abokan Pam Jonah Jang sun kammala komai tuni, har sun saya masa fam a jam’iyyar PDP
  • A shekarar 2023, watakila Pam da mahaifinsa watau tsohon gwamnan Filato su tafi majalisar tarayya

Plateau - Pam Jonah Jang wanda ‘da ne ga Sanata Jonah Jang, ya shiga cikin ‘yan siyasar da ke harin kujerar Jos Soutj/Jos East a majalisar wakilan tarayya.

A wani rahoto da ya fito a Daily Trust ta ranar Laraba, 6 ga watan Afrilu 2022, an ji cewa Pam Jonah Jang ya na kokarin bin layin mahaifinsa, Jonah Jang.

Wasu abokan Pam Jonah Jang suka gabatar masa da takardar shiga takara watau fam na jam’iyyar PDP domin ya samu damar shiga zaben fitar da gwani.

Kara karanta wannan

2023: Tambuwal da Peter Obi za su shiga labule da masu ruwa da tsaki na PDP a majalisar tarayya a yau

Rahoton ya ce an mikawa Pam Jang fam din ne a Tamarald Hotel da ke garin Jos a ranar Talata.

Dr. Dagwom Dang ya bayyana cewa sun zakulo Pam Jang ya yi takara a karkashin PDP ne domin su na bukatar wakalici mai nagarta a majalisar wakilan tarayya.

Dang da mutanensa har sun saye fam, sun mikawa Mr. Jang domin ya wakilci mutanen Jos ta kudu da Jos ta gabas saboda nuna irin imanin da suka yi a kan shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

‘Dan cikin tsohon Gwamnan Filato
Pam Jonah Jang da fam din PDP Hoto: @thestateofplateau
Asali: Facebook

“Mun dauko shi ne saboda mu na son ayi wa mutanen mazabarmu wakilci nagari a 2023.”
“Mun yi bincikenmu a kan Pam Jonah Jang, kuma mun ga ya na da halayen shugabanci da zai iya wakiltar mu a majalisar wakilan tarayya.”
“Saboda haka mu ka saya masa fam domin gudun ya yi watsi da tayin da muka kawo masa.” - Dr. Dagwom Dang

Kara karanta wannan

Yunƙurin Kisa: Ƴan Bindiga Sun Buɗe Wa Babban Ɗan Majalisar APC Wuta

Pam Jonah Jang ya yarda ya yi takara

Punch ta ce Pam Jang bai bada kunya ba, ya karbi wannan batu da aka bijiro da shi. Jang ya tabbatar da cewa abokansa sun yi masa komai, ya yarda ya shiga zabe.

“Na san aikin majalisa akwai wahala, musamman a yadda kasar mu ta ke yau, kuma a mazaba irin ta mu, amma ina sa ran zan yi bakin kokari na.”

- Pam Jonah Jang

'Ya 'yan 'yan siyasa masu takara

Mahaifin Pam Jang watau tsohon gwamna Jonah Jang Sanata ne mai wakilatar Filato ta Arewa a majalisa. Kafin nan ya yi shekaru takwas a kujerar gwamna.

A jerin wasu 'ya 'yan manyan ‘yan siyasa da mu ka fitar cewa za su yi takara a zaben 2023, akwai 'ya 'yan tsofaffin gwamnonin Sokoto da Jigawa, duk a PDP.

Mustafa Sule Lamido ya na shirin yin takarar gwamna a jihar Jigawa, yayin da Sageer Attahiru Bafarawa zai nemi takarar gwamnan Sokoto a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Ana maganar rufe Majalisa domin tursasa Shugaban kasa ya tashi-tsaye kan lamarin tsaro

Asali: Legit.ng

Online view pixel