2023: Tambuwal da Peter Obi za su shiga labule da masu ruwa da tsaki na PDP a majalisar tarayya a yau

2023: Tambuwal da Peter Obi za su shiga labule da masu ruwa da tsaki na PDP a majalisar tarayya a yau

  • Za a saka labule tsakanin Gwamna Aminu Tambuwal, Peter Obi da kuma mambobin PDP a majalisar dokokin tarayya
  • Ana sanya ran jiga-jigan na PDP za su gana ne a daren yau Talata, 5 ga watan Afrilu, da misalin karfe 9:00
  • Tuni masu neman takarar shugabancin kasar biyu suka aike da wasika kan haka zuwa zauren majalisar wakilai, wanda Gbajabiyamila ya karanto a yayin zamansu

Abuja - Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal da tsohon gwamnan jihar Anambra, za su gana da mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a majalisar dokokin tarayya a yau Talata, 5 ga watan Afrilu.

Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ne ya karanto wasikar Tambuwal da Obi wanda a ciki ne suka gabatar da bukatar tasu ta son zantawa da yan majalisar na PDP, a zauren majalisa.

Kara karanta wannan

Neman kujerar Shugaban kasa ya barka Atiku, Saraki da ‘Yan takarar PDP, kai ya rabu 3

Wasikar na dauke da sa hannun Ndudi Elumelu, shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilan, jaridar The Cable ta rahoto.

2023: Tambuwal da Peter Obi za su shiga labule da masu ruwa da tsaki na PDP a majalisar tarayya a yau
2023: Tambuwal da Peter Obi za su shiga labule da masu ruwa da tsaki na PDP a majalisar tarayya a yau Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Rahoton ya kuma nuna cewa za a yi taron ne da misalin karfe 9:00 na daren yau kuma zai gudana ne a Wuse 2 da ke Abuja.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan karanto wasikar, sai Gbajabiamila ya tambayi shugaban marasa rinjayen ko Tambuwal da Obi za su hade ne don yin takarar shugaban kasa a tare.

Da yake martani, Elumelu ya ce:

“Siyasa ce ba da gaba ba kamar yarjejeniyarku na Eagle Square."

Yayin da Obi ya ayyana aniyarsa ta takarar shugabancin kasar a 2023 a ranar 24 ga watan Maris, har yanzu Tambuwal na kan tuntuba ne kuma bai ayyana kudirinsa ba tukuna.

2023: Atiku, Wike da sauransu za su san makomarsu a yau yayin da kwamitin shiyya na PDP zai zartar da hukunci

Kara karanta wannan

Buhari ya nemi Sanatoci su tabbatar da sababbin mukamai 5 da ya nada a hukumomin gwamnati

A wani labarin, mun ji cewa ana sanya ran kwamitin rabon mukaman shugabanci na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) mai mambobi 37 zai sanar da hukuncinsa kan tsarin rabon shiyya-shiyya na jam’iyyar a zaben shugaban kasa na 2023.

Kwamitin ya shirya yin watsi da tsarin karba-karba na jam’iyyar domin ba masu takarar shugaban kasarta damar fafatawa don mallakar tikitin jam’iyyar a zaben fidda gwani da za a yi a ranakun 28-29 ga watan Mayu.

Masu takarar kujerar shugaban kasa suna ta tuntuba da kamun kafa domin tabbatar da ganin cewa hukuncin da kwamitin zai dauka bai kawo masu cikas ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel