‘Ya 'ya, mata, 'yanuwa da surukan 'Yan siyasa 9 da ke shirin yin takara a zaben 2023 a Najeriya

‘Ya 'ya, mata, 'yanuwa da surukan 'Yan siyasa 9 da ke shirin yin takara a zaben 2023 a Najeriya

  • Alamu na nuna cewa wasu daga cikin ‘ya ‘yan shahararrun ‘yan siyasar kasar nan za su bi sahunsu
  • Akwai iyalin masu mulki ko wadanda suka yi mulki a baya da za su shiga takara a zabe mai zuwa
  • Wasu na cewa an maida abin gado, yayin da magoya baya ke cewa iyalan manyan sun cancanta

Legit.ng Hausa ta kawo jerin irin wadannan mutane da ake zargin sun kwallafa ransu a kujerar siyasa:

1. Marilyn Okowa-Daramola

A jerin na mu akwai Misis Marilyn Okowa-Daramola wanda tun kwanakin baya ake rade-radin cewa za ta fito takara a zaben 2023 lokacin da wa’adin mahaifinta zai cika.

Marilyn Okowa-Daramola ‘diya ce wajen gwamnan jihar Delta watau Sanata Ifeanyi Okowa.

2. Godswill Edward

Godswill Edward wanda shi ne Mai taimakawa gwamna Ben Ayade da shawara kan harkar fina-finai da wasanni ya bayyana cewa zai nemi takarar gwamna a Kuros Riba.

Kara karanta wannan

Kan gwamnoni da jiga-jigai ya yi kwari, sun shirya yakar ‘Yan takarar Buhari a zaben APC

Surukin na tsohon shugaban kasa Goocluck Jonathan zai yi takara ne a karkashin jam’iyyar APC.

3. Ebelechukwu Obiano

A lokacin da gwamna Willie Obiano yake kan karagar mulki ne ya tabbatar da cewa Ebelechukwu Obiano za ta nemi kujerar Sanatar Anambra ta Arewa a 2023.

Da alama cewa Mai dakin Obiano, Ebelechukwu Obiano za tayi takara ne a karkashin APGA.

4. Sageer Bafarawa

Sageer Attahiru Bafarawa ya tabbatar da cewa zai nemi takarar gwamnan Sokoto a PDP mai mulki. A 2023 za ayi zaben sabon gwamna da zai gaji Aminu Tambuwal.

Mahaifinsa watau Attahiru Dalhatu Bafarawa ya yi mulki tsakanin shekarar 1999 da 2007.

5. Mustafa Sule Lamido

Fastocin Mustafa Sule Lamido sun soma yawo a jihar Jigawa. Ana kyautata zaton cewa zai jarraba sa’a wajen zama gwamna a karkashin jam’iyyar hamayya ta PDP.

Kara karanta wannan

2023: Mulkin Buhari ba komai bane face yaudara, dan takarar shugaban kasa na PDP

Mahaifinsa babban ‘dan siyasa ne wanda ya sauka daga kujerar gwamnan Jigawa a Mayun 2015.

‘Ya 'ya, mata, 'yanuwa da surukan 'Yan siyasa
Masu neman yin gado a siyasa
Asali: UGC

6. Abba Abdullahi Ganduje

Akwai rade-radi da ake tayi cewa Abba Abdullahi Ganduje zai yi takarar kujerar ‘dan majalisa mai wakiltar Dawakin Tofa/Rimin Gado/Tofa a jihar Kano.

Abba yana cikin ‘ya ‘yan gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Ganduje wanda zai sauka a shekarar badi.

7. Bello El-Rufai

Wasu sun ce Bello El-Rufai zai shiga siyasa dumu-dumu a shekarar nan inda zai nemi zama ‘dan majalisar mutanen yankin Kaduna ta Arewa a majalisar tarayya.

Bello El-Rufai shi ne babban yaron gwamnan Kaduna, yanzu haka hadimi ne na Sanata Uba Sani.

8. Abba Kabir Yusuf

Injiniya Abba Kabir Yusuf ne ya yi wa PDP takara tun a zaben 2019 a jihar Kano. Watakila Abba Gida Gida zai yi takarar gwamna wannan karo ne jam’iyyar NNPP.

Abba Yusuf suruki ne wajen tsohon gwamnan Kano watau Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Gawurtattun ‘Yan siyasa 12 da za su iya neman takarar Gwamnan jihar Kano a zaben 2023

9. Mohammed Halilu Modi

Jita-jita na yawo cewa Mohammed Halilu Modi yana da burin zama gwamnan jihar Adamawa a zabe mai zuwa na 2023, kuma ya na neman jam’iyyar APC ta tsaida shi.

Halilu Modi kani ne a wajen uwargidar shugaban kasa watau Aisha Muhammadu Buhari.

10. Baffa Namadi Sambo

Legit.ng Hausa ta da samun kishin-kishin cewa akwai yiwuwar Baffa Namadi Sambo ya gwabza da ‘dan gwamnan Kaduna wajen zama ‘dan majalisar Kaduna ta Arewa.

Namadi Sambo ya yi gwamna a jihar Kaduna kafin ya zama mataimakin shugaban kasa a 2010.

Asali: Legit.ng

Online view pixel