Bayan ya yi ikirarin bai da kudi, kungiya za ta ba Amaechi N2bn ya yi kamfe a zaben 2023

Bayan ya yi ikirarin bai da kudi, kungiya za ta ba Amaechi N2bn ya yi kamfe a zaben 2023

  • Bridge Builders Initiative For Green Nigeria ta dage cewa sai Rotimi Amaechi ya yi takarar shugaban kasa
  • Kungiyar ta ce Rt. Hon. Chibuike Rotimi Amaechi ya fi cancanta ya zama shugaban Najeriya a zaben 2023
  • Shugaban BBIGN ya ce sun ware N2bn da Ministan sufurin zai kashe a kamfe tun da ya na kukan kudi

Abuja - Wata kungiya ta ‘yan jam’iyyar APC mai mulki mai suna Bridge Builders Initiative For Green Nigeria ta na tare da Rotimi Amaechi a zaben 2023.

Jaridar Daily Trust ta ce kungiyar BBIGN ta ba Rotimi Amaechi wa’adin kwanaki 21 ya fito ya bayyanawa ‘yan Najeriya cewa zai nemi shugabancin kasa.

Bugu da kari, Bridge Builders Initiative For Green Nigeria ta ce ta adana Naira biliyan 2 saboda Amaechi ya yi takarar shugaban kasa a zaben shekarar badi.

Kara karanta wannan

Abin da wasu wadanda suka yi takara a APC suke fada, bayan sun sha kashi a zaben kasa

Shugaban kungiyar BBIGN na kasa, Mista Emmanuel Orgwu ya bayyana wannan a ranar Laraba.

Rotimi Amaechi ya fi kowa cancanta?

Da yake jawabi a sakatariyar jam’iyyar da ke birnin Abuja, Emmanuel Orgwu ya ce babu wanda ya dace da mulki bayan Muhammadu Buhari irin Hon. Amaechi.

An rahoto Orgwu yana cewa idan Amaechi ya samu mulkin Najeriya, zai daura daga inda gwamnatin Buhari ta tsaya domin ganin kasar nan ta cigaba.

Amaechi
Shugaban kasa tare da Rt. Hon. Chibuike Rotimi Amaechi Hoto: www.ripplesnigeria.com
Asali: UGC

Rashin kudi ba matsala ba ne ga Amaechi

A cewar Emmanuel Orgwu, rashin kudi ba zai kawowa Ministan sufurin tarayyar matsala a zabe ba domin sun tara abin da zai bukata wajen yakin neman zabe.

Har zuwa yanzu Amaechi bai ce zai yi takara ba, da aka yi masa tambaya kwanaki, sai ya ce masu zuga shi ya fito neman mulki a 2023, su ba shi kudin zabe.

Kara karanta wannan

Minista sukutum da guda ya tare a birnin Abuja saboda tsabar 'tsoron' Gwamnan jiharsa

Kungiyar ta Bridge Builders Initiative For Green Nigeria, ta na so kafin karshen watan Afrilun nan, Ministan ya ayyana niyyar neman kujerar shugabancin kasa.

“Mu ‘yan Najeriya mun adana kudi Naira biliyan biyu da za mu ba Chibuike Rotimi Amaechi saboda hidindimun zabe da zarar ya ce zai yi takara a 2023.”
“Saboda haka Mai girma Minista, kudi ba matsala ba ne, kuma ba zai kawo wani cikas ba.” - Emmanuel Orgwu.

Siyasar jam'iyyar PDP

Dazu mu ka samu rahoto da ya nuna gaskiyar magana ita ce har yanzu ba a tsaida ‘dan takara daga Arewa da zai gwabza da ‘yan siyasan kudu a zaben PDP ba.

Labaran da suke yawo a makon nan ba gaskiya ba ne domin Osaro Onaiwu ya ce Bukola Saraki, Aminu Tambuwal da Bala Mohammed ba su janye takararsu ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel