Rade-radin cewa Saraki, Tambuwal sun janyewa Atiku a takarar PDP ba gaskiya ba ne

Rade-radin cewa Saraki, Tambuwal sun janyewa Atiku a takarar PDP ba gaskiya ba ne

  • Maganar cewa manyan ‘yan takarar PDP sun sallamawa Atiku Abubakar a 2023 ba gaskiya ba ne
  • Osaro Onaiwu ya ce har yanzu Bukola Saraki, Aminu Tambuwal da Bala Mohammed su na takara
  • Darekta Janar na kwamitin yakin neman zaben Saraki ya ce duka ‘yan takarar sun dace da mulki

Abuja - Kwamitin yakin neman zaben Bukola Saraki ya musanya jita-jitar cewa shi da wasu masu neman takara sun hakura, sun janyewa Atiku Abubakar.

Jaridar Punch ta ce kwamitin neman takarar na 2023 ya karyata wadannan rahotanni a ranar Laraba.

Darekta Janar na wannan kwamiti, Osaro Onaiwu ya fitar da wani jawabi na musamman yana cewa wannan aika-aikar wasu ‘yan adawa ne kurum a PDP.

Osaro Onaiwu ya bayyana cewa masu yin wannan su na neman tikiti ne ta hanyar yadaran jama’a alhali kuwa kowanensu ba kanwar lasa ba ne a zabe.

Kara karanta wannan

Kada Wanda Ya Zarce Shekaru 70 Da Haihuwa Ya Tsaya Takarar Shugaban Ƙasa, Ortom

Hakan na zuwa ne bayan an ji labari cewa Bukola Saraki, Aminu Waziri Tambuwal da Bala Mohammed duk sun yarda a ba Atiku Abubakar tutan PDP.

Jawabin Osaro Onaiwu

“Hankalin mu ya zo ga wani labari da wata jaridar yanar gizo ta wallafa cewa ‘dan takararmu da kuma Aminu Tambuwal da Bala Mohammed sun janye.”
Saraki, Tambuwal da Bala
Aminu Tambuwal, Bukola Saraki da Bala Mohammed Hoto: 21stcenturychronicle.com
Asali: UGC
“Wai sun janye takararsu Atiku Abubakar wajen neman tikitin shugaban kasa a jam’iyyar PDP.”
“Wannan rahoto tsantsagoron yaudara ce da wasu suka kitsa da nufin samun tutar PDP ta hanyar yaudaran jama’a. ‘Dan takararmu ya cacanci a ba shi tuta.”

Abin da ya faru a ranar Litinin

“’Dan takararmu da sauran masu neman kujerar shugaban kasa sun hadu da Atiku a ranar Litinin ne domin sanar da shi su na shirin a tsaida ‘dan takara daya.”

Kara karanta wannan

Ba a tsame Atiku daga cikin yan takarar yarjejeniya ba, Saraki

“Kuma a wannan zaman, babu maganar cewa wani ‘dan takara ya janye. Lokaci bai yi ba da za a fara wannan magana, da za a samu an kawo wannan labari.”

A karshe 21st Century Chronicle ta rahoto Onaiwu yana cewa a cikin wadanan ‘yan takara babu wanda ya fi wani da har za a ce dole ne a sallama masa tikitin.

Fayose ya na tare da Wike a PDP

A ranar Laraba ne aka ji Ayodele Peter Fayose ya bayyana matsalar da Nyesom Wike yake da ita, amma duk da haka ya ce shi zai marawa baya a zabe mai zuwa

Bayan magoya baya sun sayawa Gwamna Nyesom Wike fam domin ya nemi takarar shugaban kasa, Ayo Fayose ya ce zai maida masu N40m da suka kashe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel