2023: Ɗan takarar da shugaba Buhari zai goyi bayan ya gaji kujerar shugaban ƙasa a APC

2023: Ɗan takarar da shugaba Buhari zai goyi bayan ya gaji kujerar shugaban ƙasa a APC

  • Bayan kammala babban taron APC na ƙasa, a halin yanzun hankula zasu koma kan zaben fitar da ɗan takarar da zai gaji Buhari
  • Ana tsammanin APC zata shirya zaɓen a cikin shekarar nan, wanda Mambobin Jam'iyya za su zaɓi wanda suke kauna
  • Rahoto ya nuna cewa ɗan takarar da APC zata tsayar zai girgiza mutane a ciki da wajen Najeriya

Abuja - Rahoton Jaridar Vanguard ya nuna cewa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, zai goyi bayan ɗan takarar da ba'a yi tsammani ba a zaben fidda gwani na Jam'iyyar APC.

A cewar rahoton, nasarar Sanata Abdullahi Adamu na zama shugaban APC na ƙasa ka iya zama wata babbar dama ga gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ko Ministan Sufuri, Chibuike Rotimi Amaechi.

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
2023: Ɗan takarar da shugaba Buhari zai goyi bayan ya gaji kujerar shugaban ƙasa a APC Hoto: @OfficialAPCNG
Asali: Twitter

A wata fira da kafar Talabijin ta Najeriya a karshen 2020, Shugaban ƙasa ya bayyana cewa zaɓinsa na wanda zai gaji kujerarsa zai girgiza yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Daga karshe, Ministan Buhari ya yi faɗi shirinsa kan takarar shugaban ƙasa a 2023

Masana harkokin siyasa sun bayyana cewa ɗan takarar da Buhari ke nufi ka iya zama wani da mutane ba su yi tsammani ba, wanda ba sananne bane a cikin jam'iyya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sabon shugaban APC na ƙasa babban ɗan a mutum shugaba Buhari ne, kuma ya ce ba zai iya aikata wani abu da zai ba Buhari kunya ba.

Kalamansa sun nuna cewa, ba zai yi ƙasa a guiwa ba wajen goyon bayan duk ɗan takarar da shugaban ƙasa ya zaɓi ya gaji kujerarsa a zaben 2023.

Wane mutum ake tsammanin Buhari zai goya wa baya?

A halin yanzun, wata majiya a cikin jam'iyya tace ayyukan Buhari da kalamansa ba su nuna wasu alamu ba game da wanda yake so ya gaje shi.

Duk da haka, majiyar ta cikin gida tace ana tsammanin Buhari zai bayyana wanda zai gaje shi gabanin zaɓen fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa a watan Mayu.

Kara karanta wannan

Shugabancin APC: Dalilin da yasa muka miƙa wuya ga ɗan takarar da Buhari ke kauna, Gwamna ya fasa kwai

A wani labarin kuma Yan bindiga sun kai mummunan hari wata Hedkwatar yan sanda a Imo, mutane yankin sun tsorata sun yi takan su

Mazauna ƙauyen sun shaida wa manema labarai cewa maharan sun shigo da karfe 3:00 na dare, kuma sun kwashe dogon lokaci yayin harin.

Wani mazaunin yankin ya ce Artabun da aka yi tsakankin dakarun yan sanda da maharan ya hargitsa mutane kamar duniya ce zata tashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel