2023: Abin Da Yasa Na Hallarci Taron Ƙaddamar Da Takarar Atiku Duk Da Cewa Nima Zan Yi Takarar, Peter Obi

2023: Abin Da Yasa Na Hallarci Taron Ƙaddamar Da Takarar Atiku Duk Da Cewa Nima Zan Yi Takarar, Peter Obi

  • Peter Obi, tsohon gwamnan Jihar Anambra ya bayyana dalilin da yasa ya hallari taron kaddamar da takarar shugabancin kasa na Atiku Abubakar
  • Tsohon abokin takarar na Atiku a 2019, wanda a yanzu shima yana neman tikitin takarar shugabancin kasa a PDP ya ce baya siyasar gaba kuma
  • Ya kara da cewa Atiku shugabansa ne, mai gidansa kuma yayansa don haka idan ya gayyace shi taro zai amsa kirar a koda yaushe

Tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, ya bayyana dalilinsa na hallartar taro inda tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya ayyana sha'awarsa na takarar shugaban kasa a zaben 2023 da ke tafe.

Da ya ke magana da Channels Television a wurin taron, tsohon abokin takarar na Atiku a zaben 2019 ya bayyana cewa shi irin siyasarsa daban ne, rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: 'Abokan Tambuwal' Sun Siya Masa Fom Takarar Shugabancin Ƙasa

2023: Abin Da Yasa Na Hallarci Taron Ƙaddamar Da Takarar Atiku Duk Da Cewa Nima Zan Yi Takarar, Peter Obi
2023: Dalilin Da Yasa Na Hallarci Taron Ƙaddamar Da Takarar Atiku Duk Da Cewa Nima Ina Son Yin Takarar , Peter Obi. Hoto: The Punch.
Asali: Twitter

Ni bana siyasar gaba, kuma Atiku mai gida na ne, in ji Peter Obi

Da aka masa tambayar dalilin da yasa ya hallarci taron, duba da cewa shima yana neman tikitin takarar shugaban kasa a PDP, Obi ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Wannan sabon siyasa ne. Ni irin siyasa ta daban ne. A wuri na, siyasa ba yaki bane. Alaka ce.
"Atiku shugaba na ne, mai gida na ne kuma yaya na ne. Idan ya gayyace ni domin hallartar wani abu, zan amsa gayyatar.
"Neman takarar shugabancin kasa baya nufin in yanke alaka ta na mutunci da abota ba.
"Ina sha'awar takara. Idan ka tuna, na saba fada, Atiku mutum ne mai hada kan al'umma. Ya yi imani da Najeriya daya. Mutumin kirki ne. Duk lokacin da ya gayyace ni wani abu, zan amsa kiran."

Kara karanta wannan

Najeriya ta fi bukata ta: Abokin tafiyar Atiku ya ayyana aniyarsa ta gaje Buhari a 2023

'Abokan Tambuwal' Sun Siya Masa Fom Takarar Shugabancin Ƙasa

A wani bangare, wata kungiya mai suna Abokan Tambuwal ta siya wa gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal fom din takarar zaben shugaban kasa a jam'iyyar PDP.

Kungiyar, karkashin jagorancin Aree Akinboro, sun siya fom din ne a ranar Alhamis a hedkwatar jam'iyyar da ke birnin tarayya Abuja, The Cable ruwaito.

PDP ta tsayar da ranar 28 ga watan Mayu domin zaben yan takarar da za su wakilci jam'iyyar a zaben na 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel