Taron gangamin APC: Gobe Juma'a muke shirin sakin sunayen wadanda muka zaba, Ahmad Lawan

Taron gangamin APC: Gobe Juma'a muke shirin sakin sunayen wadanda muka zaba, Ahmad Lawan

  • Bayan ganawa da Buhari, shugaban majalisar dattawa yace gobe zasu fitar da sunayen wadanda zasu ittifaki kai
  • Buhari ya gana da shugabannin majalisa ranar Alhamis kan taron gangamin da zai gudana ranar Asabar
  • Gwamnonin na jam’iyyar APC sun yarda su goyi bayan zabin shugaba Muhammadu Buhari ya zama shugaban jam'iyyar

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan, ya bayyana cewa jigogin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) sun yarda da yin ittifaki kan wadanda za'a zaba sabbin shugabannin jam'iyyar.

A cewarsa, gabanin taron da za'a yi ranar Asabar, zasu saki jerin sunayen wadanda akayi ittifaki kansu gobe Juma'a.

Lawan ya bayyana hakan ne bayan zaman shugabannin majalisar dokokin tarayya da shugaba Muhammadu Buhari ranar Alhamis a fadar Aso Villa, rahoton ChannelsTV.

Yace:

"Muna sa ran ittifaki kan wadanda zamu zaba matsayin shugabannin jam'iyyar, shirye muke da samar da jerin wadanda za'a zaba."

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Fayemi ya yi watsi da batun goyon bayan yan takarar da Buhari ke so

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Taron gangamin APC
Taron gangamin APC: Gobe Juma'a zamu muke shirin sakin sunayen wadanda muka zaba, Ahmad Lawan Hoto: @NGRSenate
Asali: Facebook

Gwamnonin na jam’iyyar APC sun yarda su goyi bayan Sanata Abdullahi Adamu ya zama shugaban APC na kasa.

Tun tuni Muhammadu Buhari ya nuna cewa Abdullahi Adamu yake sha’awar ya rike jam’iyya. Wannan matakin ya nemi ya jawo sabani tsakanin ‘yan APC.

A karshen zaman da aka yi na ranar Laraba a Aso Rock, an cin ma matsaya cewa gwamnoni za su ba Sanatan duk goyon bayan da ake bukata.

Dalilin da yasa muka miƙa wuya ga ɗan takarar da Buhari ke kauna, shugaban kwamitin labaran taron gangamin APC

Gwamnan jihar Nasarawa kuma shugaban kwamitin Midiya na babban taron APC na ƙasa, Abdullahi Sule, ya yi bayanin abin da yasa gwamnoni suka amince da zaɓin Buhari.

Tribune Online ta rahoto gwamnan na cewa Shugaba Buhari na goyon bayan tsohon gwamnan Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu, ya zama shugaban APC na gaba.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: 'Abokan Tambuwal' Sun Siya Masa Fom Takarar Shugabancin Ƙasa

A ranar Asabar 26 ga watan Maris, 2022, APC zata gudanar da babban taronta na ƙasa wanda zata zaɓi shugabanninta.

Da yake jawabi ga manema labarai game da shirin da kwamitinsa ya yi, Gwamna Sule ya ce masu shakku kan zabin Buhari sun amince ne saboda girmamawan da Buhari ke samu daga masu faɗa a ji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel