Hamshakan ‘Yan adawan siyasa 23 da za su gwabza a zaben shugabannin APC a gobe
- FCT, Abuja - A ranar Asabar dinnan, 26 ga watan Maris 2022 ne za a san su wanene za su rike mukamai a matakin jam’iyyar APC mai mulki na kasa
- Daily Trust ta bi yadda wannan zaben shugabannin zai kasance, ta kawo wasu gawurtattun ‘yan adawan siyasa da za su nunawa junansun karfinsu
- Daga sabanin 'Yan G7 da Ganduje zuwa tsohon fadan Rotimi Amaechi da Magnus Abe, mun kawo duk wasu rigingimu da ba a gama shawo kansu ba
1. Lai v Abdulrazaq
An dade ana rikici tsakanin Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed da gwamnan jihar Kwara, Abdulrazaq Abdulrahman a gidan jam’iyyar APC.
2. Amaechi v Abe
Ministan sufuri na kasa, Rotimi Amaechi da Sanata Magnus Abe su na cikin wadanda za sus an matsayarsu a jam’iyyar APC bayan zaben da za ayi a gobe.

Kara karanta wannan
Maye: Abu 5 da ya kamata ku sani game da Abdullahi Adamu, mutumin da Buhari ya zaba matsayin shugaban APC
3. Aregebsola v Oyetola
Jaridar ta kawo sabanin Ogbeni Rauf Aregbesola da magajinsa, gwamna Gboyega Oyetola a cikin daya daga cikin mafi munin gwabzawar da za ayi a zaben APC.
4. Ganduje v Shekarau
Ba sabon labari ba ne cewa ba a jituwa Sanata Ibrahim Shekarau da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje. Zaben shugabannin zai nuna wanene zai samu iko da Kano.
5. Amosun v Abiodun
Kamar a jihar Ondo, babu zaman lafiya tsakanin kusoshin APC, Sanata Ibikunle Amosun da wanda ya gaje shi a Ondo, Dapo Abiodun, ‘yan siyasar za su gwabza.
6. Yari v Marafa v Matawalle
Daga cikin rikicin cikin gidan da suka yi kamari a APC akwai na Abdulaziz Yari da Kabiru Matafa da kuma Gwamna Bello Matawalle wanda ya shigo APC daga baya.

Kara karanta wannan
‘Ya 'ya, mata, 'yanuwa da surukan 'Yan siyasa 10 da ke shirin yin takara a zaben 2023

Asali: UGC
7. Wammako v Gada
Legit.ng Hausa ta fahimci rigimar Sanata Aliyu Magatakarda Wammako da Sanata Abubakar Gada yana cikin wadanda har yanzu ba a shawo kansu a APC ba.
8. Aleiro v Malami
Ana zargin har zuwa yanzu babu zaman lafiya tsakanin Sanata Mohammed Adamu Aleiro da Abubakar Malami wanda ake tunanin ya tare da gwamna Atiku Bagudu.
9. Ngige v Uba
Zaben gwamnan da aka yi a Anambra ya nuna gidan jam’iyyar APC ba a dunkule yake ba. A zaben shugabannin, Dr. Chris Ngige zai nemi ya nunawa Ifeanyi Uba iyakarsa.
10. Keyamo v Omo-Agege
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo Agege da karamin Ministan kwadago, Festus Keyamo SAN za su so su samu iko da kujerun NWC na yankinsu a APC.
11. Okorocha v Uzodinma
Ba zai yiwu ayi batun takun sakar da ake yi a APC ba tare da kawo Sanata Rochas Okorocha da gwamnansa, Hope Uzodinma ba. Za su kara da juna a zaben shugabannin.

Kara karanta wannan
Ana daf da zaben shugabannin APC, Buhari ya hadu Tinubu da wadanda suka kafa jam’iyya
Rikicin APC Kwara
Kwanakin baya kun ji labari cewa Alhaji Lai Mohammed da kuma Sanata Gbemisola Saraki sun hurowa gwamna AbdulRahman AbdulRazaq wuta a APC taKwara.
Bashir Bolarinwa shi ne ke jagorantar bangaren ‘yan tawaren da ke tare da Lai a reshen jihar Kwara yayin da Fagbemi Adeniran yake da goyon bayan gwamna.
Asali: Legit.ng