Lai, Gbemisola da Abdulrazaq su na yakin karbe Jam’iyyar APC a Jihar Kwara

Lai, Gbemisola da Abdulrazaq su na yakin karbe Jam’iyyar APC a Jihar Kwara

- Lai Mohammed da Gbemisola Saraki sun huro wa AbdulRahman AbdulRazaq wuta

- Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq bai goyon bayan shugabancin Bashir Bolarinwa

- Wadanda basu tare da Gwamnan su na goyon bayan Bolarinwa ya rike APC a jihar

Ministoci biyu masu ci a gwamnatin Muhammadu Buhari Lai Mohammed da Gbemisola Saraki za su fafata da Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq a APC.

Rahotanni daga Vanguard sun bayyana cewa Ministocin na Kwara suna rikici ne da Mai girma gwamnan jihar kan wanda zai rike shugabancin jam’iyya a gida.

Lai Mohammed da Gbemisola Saraki da ma wasu jiga-jigan APC sun sha alwashin ganin bayan AbdulRahman AbdulRazaq da ya ke ja da Hon. Bashir Bolarinwa.

Gwamnan ya na neman ganin an ki tsaida Bashir Bolarinwa a matsayin shugaban rikon-kwarya na jam’iyyar APC a jihar Kwara, bayan an sauke duka shugabanni.

KU KARANTA: Gwamnan Kwara ya rusa gidan danginsu Saraki

Wadannan kusoshin ‘yan siyasa su na ganin yunkurin gwamnan ya saba doka, kuma bai dace ba.

Akogun Iyiola Oyedepo, wani jagoran APC a Kwara, ya yi magana da ‘yan jarida, inda ya soki yunkurin da gwamnan ya ke yi na hana Bolarinwa rika jam’iyya.

Mista Akogun Iyiola Oyedepo ya yi magana ne tare da Oladimeji Mustapha da Ayo Obisesan a gefensa, wadanda suke wakiltar Lai Mohammed da Gbemisola Saraki.

Dukkanin bangarorin jam’iyyar APC a Kwara sun halarci wannan taro ban da bangaren gwamna Abdulrahman AbdulRasaq wanda ba ya tare da Ministsocin tarayyar.

KU KARANTA: Bukola Saraki ya ba 'Yan siyasar Najeriya shawara

Lai, Gbemisola da Abdulrazaq su na yakin karbe Jam’iyyar APC a Jihar Kwara
Gwamnan Jihar KwaraAbdulRahman AbdulRazaq Hoto: thisdaylive.com
Source: Twitter

Akogun Oyedepo ya nuna damuwarsa na cewa AbdulRasaq bai gayyaci Hon Bashir Bolarinwa wajen nadin shugabannin rikon-kwarya da za ayi a birnin Abuja ba.

Kwanakin baya kun ji cewa wata al'ummar kudancin jihar Kwara, ta bakin kungiyar dattawan yankin watau KSCF sun gabatar da bukatunsu na cewa suna so su rabe.

Wadannan mutanen suna bukatar a hada su da yarbawan yankin Kogi ga yan'uwansu dake kudu maso yammacin Najeriya a maimakon a cigaba da barinsu a jihar Kwara.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel