Rikicin APC a Sokoto: Kotun Daukaka Kara ta soke hukuncin ba tsagin Sani nasara

Rikicin APC a Sokoto: Kotun Daukaka Kara ta soke hukuncin ba tsagin Sani nasara

  • Kotun daukaka kara ta zartar da hukunci yayin da rikicin shugabanci ya dabaibaye jam'iyyar APC a jihar Sokoto
  • A ranar Alhamis, 24 ga watan Maris, kotun daukaka karar ta soke hukuncin babbar kotun Abuja da ta baiwa tsagin Sani shugabancin jam'iyyar
  • Ta ce kotun Abuja bata da hurumin sauraron wani al'amari da ya faru a jihar Sokoto

Abuja - Wata kotun daukaka kara da ke zama Abuja, ta soke wani hukuncin babbar kotun birnin tarayya da aka yanke a ranar 16 ga watan Disamba 2021, wanda ya tabbatar da bangaren Mainasara Sani a matsayin shugabannin APC a jihar Sokoto.

Jam’iyyar reshen jihar ta fada rikici yayin da bangarori biyu ke ikirarin sune shugabanni.

Daya daga cikin bangarorin APC a jihar na biyayya ga tsohon gwamnan jihar, Aliyu Wamakko, yayin da dayar ke biyayya ga Sanata Abubakar Gada, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Fayemi ya yi watsi da batun goyon bayan yan takarar da Buhari ke so

Rikicin APC a Sokoto: Kotun Daukaka Kara ta soke hukuncin ba tsagin Sani nasara
Rikicin APC a Sokoto: Kotun Daukaka Kara ta soke hukuncin ba tsagin Sani nasara Hoto: Thisday
Asali: UGC

Tsagin Wamakko ya samar da Isa Sadiq Achida a matsayin shugaban jam’iyyar bayan kammala taronta na jiha.

Sai dai kuma, Atoni Janar na tarayya kuma ministan shari’a, Abubakar Malami ya ayyana Mainasara Sani a matsayin sahihin shugaban jam’iyyar na jihar a taron jihar da tsagin Sanata Gada ya shirya a jihar.

Da farko babbar kotun birnin tarayya ta ki amincewa da bukatar da tsagin Wamakko ya gabatar na a yi watsi da hukuncin da ta yanke a baya kan takaddamar taron jam’iyyar a jihar.

Sai dai kuma tsagin Wamakko ya tunkari kotun daukaka kara don daukaka kara kan hukuncin babbar kotun.

Da yake zartar da hukunci kan lamarin, alkalin kotun daukaka kara, Haruna Simon Tsammani, ya soke hukuncin babbar kotun FCT saboda ba a yankin ta bane.

Kara karanta wannan

Abdulaziz Yari: Zan yi amfani da kwarewata ta siyasa na daidaita barakar da ke cikin APC

Justis Tsammani ya bayyana cewa babbar kotun FCT bata da hurumin sauraron wani lamarin da ya afku a jihar Sokoto, rahoton Daily Post.

Tsammani ya ce:

“Wannan kotu da kotun koli sun sha bayar da sanarwa game da lamarin da ya shafi yankin. Kawo irin wadannan shari'o'in, kuna neman mu zauna kan namu hukuncin ne.
“Ya kamata mu sani cewa a inda wani al’amari ya faru, a nan ne ya kamata a magance shi.
“Ta yaya wani zai taso daga Sokoto har Abuja kan wani al’amari da ya kamata a yi magana a can? Ire-iren wadannan tsare-tsare ne muke fushi da su kuma hatta da Kotun Koli ta na fushi da shi.
“Na kuma soke karar ne kan rashin hurumi.
“Babbar kotun tarayya da ke Abuja tana da hurumin sauraron lamuran da suka taso daga Abuja ne kawai. Babbar kotun birnin tarayya bata da hurumin sauraron lamarin.
"An soke duk wani batu ciki harda yanke hukunci da aka yi babbar kotun.”

Kara karanta wannan

Sauya sheka: Kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan karar da ke neman a tsige Dogara

Dalilin rabuwar kan sauran jam'iyyun siyasa: Babu jam'iyyar da ke da uba kamar Buhari, inji Ahmad Lawan

A gefe guda, shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya yi magana kan ko me ke ya jawo rashin hadin kan sauran jam’iyyun siyasa.

Lawan a ranar Alhamis, 24 ga watan Maris, ya lura da cewa hakan na iya kasancewa saboda basu da uba kamar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Jigon na APC ya bayyana Buhari a matsayin uba, inda ya kara da cewa shugaban kasa yana tabbatar da an sasanta rashin jituwa kuma kowa ya samu kwanciyar hankali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel