Shirin taron gangami: Kwamiti ya tantance jiga-jigai 7 da ke neman kujerar shugabancin APC

Shirin taron gangami: Kwamiti ya tantance jiga-jigai 7 da ke neman kujerar shugabancin APC

  • Gabannin babban taron APC na kasa, karamin kwamitin tantance yan takarar shugabancin jam'iyya na kasa da Masari ke jagoranta ya shiga aiki gadan-gadan
  • Zuwa yanzu, kwamitin ya tantance dukkanin yan takarar shugabancin jam'iyyar na kasa da na mataimaka
  • Sai dai kuma wasu masu neman mukaman jam'iyyar sun koka da yadda shirin tantancewar ke tafiyar hawainiya yan kwanaki kafin taron

Abuja - Kwamitin tantancewa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da Gwamna Aminu Bello Masari ke jagoranta, ya tantance daukacin yan takarar shugabancin jam’iyyar na kasa su bakwai gabannin babban taronta da za a yi a ranar Asabar.

An gudanar da shirin tantance su ne a masaukin Gwamnan Katsina da ke babbar birnin tarayya Abuja.

Daily Trust ta rahoto cewa an fara shirin tantance yan takarar shugabancin jam’iyyar ne a daren ranar Talata har zuwa ranar Laraba inda aka tantance tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu da sauransu.

Kara karanta wannan

Gwamnonin APC: Duk wanda Buhari ya zaba a taron gangamin shi za mu marawa baya

Babban gangamin taron APC: An tantance Adamu, Al-Makura, Akume da Yari yayin da wasu suka koka
Babban gangamin taron APC: An tantance Adamu, Al-Makura, Akume da Yari yayin da wasu suka koka Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Majiyoyin jam’iyyar da ke a wajen tantancewar sun ce dukkanin yan takarar da suka siya fom din takara sun hallara kuma cewa babu wanda aka tabbatar da rashin cancantarsa har zuwa lokacin kawo wannan rahoton.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Masu neman takarar sune; tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Tanko Al-Makura; sanata mai wakiltan Neja ta gabas, Sani Musa; tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari.

Sauran sune ministan ayyuka na musamman da harkokin gwamnati, Sanata George Akume; tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu; Turaki Ilorin, Saliu Mustapha da Saidu Etsu.’

Karamin kwamitin da Masari yake jagoranta yana tantance mataimakan shugaban jam’iyya a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Bayan tantance yan takarar kujerar shugabancin jam’iyyar, kwamitin ya kuma tantance yan takarar mataimakin shugaban jam’iyyar (arewa da kudu) kafin ya fara na mataimakan shugabannin.

Wadanda ke takarar mataimakin shugaba na kasa (arewa) sune; Sunny Sylvester Moniedafe (Jagaban Jimeta); tsohon gwamnan jihar Bauchi, Isa Yuguda; tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara da Sanata Abubakar Girei wadanda duk an tantance su.

Kara karanta wannan

Gudun rikici, Shugaba Buhari zai gana da yan takarar kujerar shugaban APC

A halin da ake ciki, wasu yan takara da ke neman mukaman siyasa a babban taron jam’iyyar na kasa sun koka kan yadda ake tafiyar hawainiya wajen aiwatar da shirin.

Wasu yan takara da ke jiran a tantance su a wajen shirin sun fada ma Daily Trust cewa sun kasance a wajen tun safe amma ba a tantance su ba tukuna.

Shugabancin APC na kasa: Mika kujera wata shiyya ba ka'ida bane, Abdulaziz Yari

A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Abdullazez Yari, ya ayyana cewa karba-karba ya saba kundin tsarin mulki a jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Yari ya kuma bayyana cewa shi ya riga ya siya fom din takarar kujerar shugaban jam’iyyar gabannin babban taron ranar Asabar, 26 ga watan Maris.

Leadership ta rahoto cewa Yari wanda ya bayyana hakan yayin da ya gana da masu ruwa da tsaki na APC a majalisar dattawa da kuma neman goyon bayansu, ya ce ya zama dole jam’iyyar ta samar da wanda zai iya.

Kara karanta wannan

2023: Jam’iyyun siyasa 5 sun shirya mikawa Tinubu tikitin takarar shugaban kasa – Kungiyoyin arewa

Asali: Legit.ng

Online view pixel