Kaduna 2023: Dattijo Ya Kai Wa Sarkin Zazzau Ziyara, Yana Neman Tubarraki

Kaduna 2023: Dattijo Ya Kai Wa Sarkin Zazzau Ziyara, Yana Neman Tubarraki

  • Wani dan takarar gwamnan Jihar Kaduna, Muhammad Sani Abdullahi, wanda aka fi sani da Dattijo, ya kai wa Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli Ziyara
  • Majiyoyi sun bayyana cewa akwai jinin sarauta tattare da Dattijo idan aka bi tsatson sa ta marigayi Sarkin Zazzau, Alhaji Dalhatu Usman Yero
  • Yayin da ya kai ziyarar kamfen din ta kwana biyu, Dattijo ya kai ziyara duk ofisoshin jam’iyyar APC da ke karamar hukumar Zaria

Kaduna - Dan takarar gwamnan Jihar Kaduna, Muhammad Sani Abdullahi wanda aka fi sani da Dattijo ya kai ziyara ga Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli har fadar sa, yayin da ya ke ci gaba da kamfen, rahoton Daily Trust.

Kaduna 2023: Dattijo Ya Kai Wa Sarkin Zazzau Ziyara, Yana Neman Tubarraki
Kaduna 2023: Dattijo Ya Kai Wa Sarkin Zazzau Ziyara, Yana Neman Albarka. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Dattijo yarima ne ga masarautar Zazzau idan aka bi tsatson sa ta marigayi Sarkin Zazzau, mai martaba Alhaji Dalhatu Usman Yero, na Fulato-Borno da ya mulka Zazzau.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Tsaro ya tabarbare a Imo, Buhari ya ce a tura karin jami'ai da makamai

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin da ya je kamfen din na kwana biyu, Dattijo ya samu tubarraki da kuma addu’o’i daga Sarkin Zazzau a fadarsa.

Sarkin Zazzau ya yaba da halayen dan takarar

Sarkin ya yaba da halayen da dan takarar ya ke da su na shugabanni na kwarai, inda ya shawarce shi akan kasancewa mai da’a a gaba daya kamfen din shi tare da girmamawa ga sauran ‘yan takara masu neman kujera irin tasa a jam’iyyu daban-daban.

Tun farko, Dattijo ya nemi goyon baya ga ‘yan uwan sa da ke Amaru, asalin wurin da zuri’ar su Walin Zazzau, Injiniya Aminu Umar yake, yayin da suka dinga yi masa addu’o’i da fatan alheri.

Har ila yau, Dattijo ya kai ziyara ga gundumar Kwarbai A da kuma ofisoshin jam’iyyar APC da ke karamar hukumar Zaria, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Rikicin APC: Abubuwan da Gwamna Buni da Bello suka tattauna a ganawarsu

Dattijo ya nemi goyon bayan shugabanni daga gudumomin 13 na jam’iyyar da ke Zaria.

Shugaban jam’iyyar ta Zaria ta nuna masa goyon baya

Shugaban jam’iyyar APC ta karamar hukumar Zaria, Hajiya Rakiya Adamu, a nata jawabin cewa ta yi:

“Dattijo dan mu ne, don haka wannan aikin mu ne.
“Za mu jagoranci kamfen a Zaria don ya samu nasarar lashe kujerar gwamna.”

Har ila yau, Dattijo ya nemi goyon bayan shugaban karamar hukumar Zaria, Honarabul Aliyu Idris Ibrahim da kuma dan majalisa mai wakiltar mazabar Zaria Birni a majalisar jihar, Honarabul Suleiman Dabo, Wakilin Birnin Zazzau da sauran kusoshi na jam’iyyar da ke karamar hukumar Zaria.

Duk wannan yawon kamfen din da Dattijo yake yi, yana neman kujerar gwamnan Jihar Kaduna ne.

Tsohon Shugaban NEMA, Sani Sidi, Ya Koma PDP Bayan Shekaru 3 A Jam'iyyar APC

A wani labarin, Tsohon darekta janar na National Emergency Management Agency (NEMA), Alhaji Mohammed Sani Sidi, ya bar jam’iyyar APC daga PDP, Nigerian Tribune ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamna Buni ya diro Najeriya daga Dubai, ya yi jawabi kan abinda ya faru bayan ya karbi ragamar APC

Sidi ya bayyana kudirin sa ne a ofishin PDP na mazabar Kaduna ta tsakiya a karshen makon nan.

Kamar yadda ya ce da tarin magoya bayan sa wadanda suka je ofishin cewa:

“duk wanda ya bar gida, gida ya bar shi. Ina farin cikin dawowa gida.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel